Yanzu-yanzu: An ji karan tashin wani abin fashewa a jihar Kano, gwamnati ta ce tukunyar Gas ce

Yanzu-yanzu: An ji karan tashin wani abin fashewa a jihar Kano, gwamnati ta ce tukunyar Gas ce

Jama'an gari sun ji karan tashin wani fashewa a jihar Kano.

Wannan abu ya faru ne a unguwar Badawa Layout.

Hadimin gwamnan Kano na yada labarai, Salihu Tanko Yakassai, ya bayyana cewa jami'an DSS sun dira wajen kuma babu wani abin tashin hankali.

A cewarsa, tukunyar Gas ce ta fashe a cikin wani gida.

"Muna sanar da daukacin jama'ar Kano cewa tashin abin fashewar da akace ya faru a Badawa Layout sakamakon fashewar tukunyar gas ce, ba wani barazana bane na tsaro," Yakassai yace.

"Jami'an tsaro musamman DSS na wajen kuma babu wani abin tashin hankali."

Asali: Legit.ng

Online view pixel