Ku binciko bata-garin da ke cikin ku, Obaseki ya faɗawa makiyaya
- Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya bukaci makiyaya fulani da ke yankinsa su rika tona bata gari daga cikinsu
- Gwamnan ya yi wannan kirar ne a karamar hukumar Ovia ta jihar yayin ziyarar gani da ido bayan rikici da ta faru
- Obaseki ya yi kira ga yan Nigeria su dena saka siyasa a batun rikicin makiyaya da manoma suyi aikin ganin an samu zaman lafiya
Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya umurni makiyaya Fulani da ke jiharsa su zakulo bata garin da ke jiharsu domin idan suna son zaman lafiya, inda ya kuma gargadi kan cewa a dena jefa siyasa cikin rikicin makiyaya da manoma.
Ya bayyana hakan ne yayin ziyarar gani da ido na tsaro da ya kai a karamar hukumar Ovia ta Kudu a jihar, Daily Trust ta ruwaito.
Gwamnan, wanda ya danganta tattakin da makiyaya ke yi zuwa wurare daban-daban da dumaman yanayi ya yi kira ga yan Nigeria su binciko hanyoyin da za su sulhuta makiyaya da manoman a maimakon siyasantar da rikcin.
DUBA WANNAN: Hotunan hatsabibin mai garkuwa da aka kama yayin da ya tafi karbar kuɗin fansa
"Akwai hasashe game da rikicin makiyaya musamman a dandalin sada zumunta cewa makiyayan da suka zo daga jihohin da ke makwabtaka da mu bata gari ne.
"Amma muna da hujojji da ke nuna yan bindiga da ke basaja a matsayin makiyaya suna daga cikin masu garkuwa da aikata laifuka.
KU KARANTA: 'Yan bindiga sun tare motar ɗaukan gawa, sun yi awon gaba da ƙanin mamacin
Ya ce,"Duk da cewa muna fuskantar abinda ya haifar da rikici, matsayin mu shine na magance lamarin ba siyasantar da shi ba. Ya kamata mu amince da juna mu zauna lafiya."
A bangarensa, sarkin fulanin garin Muhammadu Buhari ya yi kira da cewa a gudanar da bincike kan zargin kashe kashe inda ya kuma bukaci a tattara bayanai da sunayen makiyaya don gano masu laifin.
A wani labarain daban, babban malamin Kano, Shaikh Abduljabbar Nasir Kabara ya ce rufe masallacinsa da hana shi yin wa'azo da gwamnatin jihar ta yi "zalunci ne", kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.
Malamin ya ce gwamnatin da kanta, ta bakin kwamishinan ilimi na jihar, ta tabbatar da cewa abinda ake yi masa zalunci ne amma ta dakatar da shi ba tare da bashi damar ya kare kansa ba.
Abdul-jabbar ya yi wannan jawabin ne biyo bayan rufe masallacinsa da ke makarantarsa da gwamnatin Kano ta yi a ranar Laraba gami da hana saka karuntunsa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta na jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng