NPF: IGP bai bayar da N2bn don a kara masa wa'adi ba, zai shigar da kara kotu
- Rundunar 'yan sanda ta karyata rahoton da wata kafar yada labarai ta watsa akan IGP Adamu, babban rundunar 'yan sanda
- Jaridar SaharaReporters ta wallafa cewa IGP Adamu ya bayar da cin hancin N2bn domin a kara masa wa'adi
- Kakakin rundunar 'yan sanda, Frank Mba, ya karyata rahoton tare da sanar da cewa IGP Adamu zai nemi hakkinsa a kotu
Mohammed Adamu, Insifeta Janar na rundunar ƴan sanda (IGP), bai biya N2bn domin a tsawaita wa'adin muƙamin sa na IGP ba, cewar mai magana da yawun rundunar yan sanda na kasa, Frank Mba a ranar Litinin.
Mba ya bayyana cewa shugaban ƙasa ne kawai ya ke da alhakin kara wa'adin muƙamin IGP, kuma shi ɗin ne ya ga dama ya kara ba wai cin hanci ne aka bayar ba, kamar yadda TheCable ta rawaito.
A ranar Litinin ne wa'adin Adamu ya ke karewa tare da yin ritaya daga aiki bayan da ya shafe shekaru 35 yana aikin gwamnati, wannan dai wata doka ce daga cikin kundin mulkin kasar Nigeria na yin ritaya bayan wa'adin aikin shekaru 35.
KARANTA: FG zata samar da wasu sabbin makarantu na musaman don koyar da ilimi a zamanance
Sai dai, IGP Adamu ya damu sahalewar shugaban kasa Muhammadu Buhari na ya ci gaba da aiki na tsawon watanni uku nan gaba, inda kuma daga bisani ne rahotanni suka ci gaba da yawo a kafofin sada zumunta na cewar Adamu ya biya cin hanci ne domin a kara wa'adin muƙamin sa.
Da ya ke martani kan waɗannan rahotanni, mai magana da yawun rundunar yan sandan, a cikin wata sanarwa ya ce, "Rundunar yan sanda na na amfani da wannan damar don sanar da jama'a cewar IGP bai biya kudi don kara wa'adin muƙamin sa ba.
"Kara wa'adin muƙamin ya biyo bayan ganin dama da sahalewar shugaban kasa ne kawai.
KARANTA: Fahimta Fuska: Ganduje ya shirya muhawara tsakanin Abduljabar da manyan Malaman Kano
"Batun cewa wai IGP bai yi bukin kara wa'adin muƙamin na sa ba, wannan wani al'amari ne na dama, amma dai muhimmancin kara wa'adin ya rataya ne kan aiki Tukur domin sauke nauyin da ya rataya a wuyan sa."
Sifeta Janar na rundunar ya ce rundunar yan sanda a karkashin shugabancin sa ta jajurce wajen inganta tsaron dukiya da rayukan al'umma."
A baya Legit.ng ta rawaito cewa gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya karbi bakuncin wata tawagar da ta dauki alhakin yin wa'azi domin shiryar da 'yan bindiga.
A jawabin da ya gabatar yayin karbar tawagar, Tambuwal ya sanar da su cewa matsalar tu'ammali da miyagun kwayoyi na kara rura wutar rashin tsaro.
Tambuwal ya bayar da labarin da wani gwamna ya bashi dangane da abinda ya faru har ya san cewa matan Fulani na safarar miyagun kwayoyi ga 'yan ta'adda.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng