Rashin saka takunkumi: Kotu ta yankewa mutane 100 hukunci a Abuja

Rashin saka takunkumi: Kotu ta yankewa mutane 100 hukunci a Abuja

- Gwamnati ta tashi tsaye domin fara tilasta masu kunnen kashi wajen bin sabuwar dokar da shugaba Buhari ya zartar

- A makon jiya ne shugaban Buhari ya rattaba hannu akan sabuwar dokar tsare mutum na wata shida akan kin saka takunkumin fuska

- Sai dai, Buhari ya sha suka da raddi bayan ganin hotonsa a cikin jama'a ba tare da takunkumin fuska ba

Wata kotu ta tafi da gidanka, a Abuja, birnin tarayya, ta zartar da hukuncin biyan tara akan wasu mutane 100 da aka samu da laifin karya dokokin kiyaye yaduwar kwayar cutar korona.

An kama mutane ne, maza da Mata, a sassan Abuja bayan samunsu da laifin kin saka takunkumin fuska a cikin jama'a, kamar yadda BBC Hausa ta rawaito.

Kwamitin Kar ta kwana na yaki da cutar korona ne ya kai samame a lungu da sako na Abuja domin kama mutanen da ke cikin jama'a amma basa bin dokar dakile yaduwar annobar korona ta hanyar saka takunkumi ba.

KARANTA: An kama matasan da ke dillancin hotuna da bidiyon tsiraicin 'yammatan Kano a yanar gizo

Ministan birnin tarayya Abuja, Muhammed Bello, shine ya kafa kwamitin bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu akan sabuwar dokar yaki da yaduwar kwayar cutar korona.

Rashin saka takunkumi: Kotu ta yankewa mutane 100 hukunci a Abuja
Rashin saka takunkumi: Kotu ta yankewa mutane 100 hukunci a Abuja
Asali: Twitter

A karkashin sabuwar dokar, za'a zartar da hukuncin daurin wata shiga ga duk wanda aka samu da shiga cikin jama'a ba tare da takunkumin fuska ba.

KARANTA: Obasanjo: Akwai banbanci a tsakanin Buharin yanzu da wanda na sani a baya

Jami'an kwamitin sun tattaro mutanen tare da jibgesu a filin taro na 'Eagle Square, kafin daga bisani a yanke musu hukunci bayan sun amsa lafinsu.

Alkalin kotun, Idayat Akani, ya yi afuwa ga mutanen ta hanyar cin tarar kowannesu dubu biyu tare da yi musu gargadin cewa su tabbatar wannan ya zama na karshe.

Ta yi musu tunin cewa doka ta bata ikon tsare mutum a gidan gyaran hali na tsawon wata shida idan aka same shi da laifin kin saka takunkumin fuska a cikin jama'a.

A baya bayan nan ne Legit.ng ta rawaito cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu akan dokar kariya daga cutar coronavirus da ke tilasta amfani da takunkumin fuska.

Dokar ta tanadi tara ko daurin wata shida ko gaba daya biyun ga duk wanda ya karya dokar.

Amma a karshen mako, an ga shugaban kasar yana tattaunawa da wasu gwamnonin APC a wajen sabunta rajistar sa ta jam'iyyar APC a Daura ba tare da sanya tukunkumin ba.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel