Wike ya ce yan adawa ne ke yada fostocin yakin neman zaben sa

Wike ya ce yan adawa ne ke yada fostocin yakin neman zaben sa

- Gwamna Nyesome na jihar Rivers Wike ya ragargarji masu adawa da gwamnatinsa a jiharsa

- Gwamnan ya ce wasu daga cikin yan adawa ne suka yada fastocin yakin neman zaben shugabancin kasarsa a wasu jihohi

- Gwamnan, ya shaida cewa, baya sha'awar tsayawa takara a babban zabe mai zuwa na shekarar 2023

Dangane da jita-jitar da ake yadawa game da takarar shugabancin kasarsa a 2023, gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike ya bayyana cewa ba shi da sha'awar tsayawa takara a babban zabe mai zuwa.

PM News ta ruwaito a wata tattaunawa da aka yi a gidan talabijin na Channels a Port Harcourt, Wike ya ce yan adawar sa ne suka shirya yadda fostocin yakin neman zaben sa suka dinga yawo a Abuja satin da ya gabata, wanda ya janyo zargin cewa yana neman kujerar lamba daya a kasa.

Wike ya ce yan adawa ne ke yada fostocin yakin neman zaben sa
Wike ya ce yan adawa ne ke yada fostocin yakin neman zaben sa. Hoto: @GovWike
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: EFCC ta kama Shugaban Jami'ar Tarayya ta Gusau kan almundahar kwangilar N260m

Legit.ng ta ruwaito cewa gwamnan ya ce duk da yana da yancin neman takarar, abin da ke gaban shi yanzu shi ne kawo ci gaban dimokradiyya ga al'ummar Rivers.

Ya ce:

"Daga Disambar shekarar da ta gabata zuwa yanzu, muna ta kaddamar da ayyuka. To mutane na ganin cewa da irin ayyukan da muke yi, ina da niyyar tsayawa takarar shugabancin kasa ne."

Wike ya kuma ce bayan kwaskwarimar da majalisa ta yi wa dokar zabe, ba zai yi daidai ba a yi zabe ta ba tare da amfani da card reader wurin tabbatar da ingancin kuri'un da aka kada.

Ya ce mafi yawancin yan majalisar suna mayar da hankulansu ne kan batun yadda za su zarce a zabe don haka sukan yi gyarar dokar zaben ne a lokacin da zai amfane su da jam'iyyunsu.

Gwamnan ya kara da cewa:

"Mene yasa shugaban kasa ya ki saka hannu kan dokar yiwa dokokin zaben garambawul, saboda mene? Saboda APC ta fada wa shugaban kasa cewa idan ya saka hannu a kan dokar, zai iya fadi zabe. Don haka, kada ka saka hannu. Don haka shugaban kasar bai saka hannu ba."

A wani labarin daban, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya goyi bayan Muhammadu Buhari a shekarar 2015 duk da cewa ya san 'bai san komai ba' Olagunsoye Oyinlola, tsohon gwamnan jihar Osun ya ce.

Mista Oyinlola ya yi bayanin cewa Mista Obasanjo ya yanke shawarar goyon bayan Mista Buhari ne saboda takaicin gwamnatin Goodluck Jonathan.

Duk da cewa (shi) Obasanjo ya san cewa dan takarar na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ba zai iya tabuka wani abin azo-a-gani ba, amma duk da haka ya goyi bayansa bayan wasu jiga-jigan yan Najeriya sun matsa masa lamba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel