Kotu ta bada umarnin a tsare Mai shekara 29 da ake zargi da laifin fyade

Kotu ta bada umarnin a tsare Mai shekara 29 da ake zargi da laifin fyade

- Kotu ta bada umarni a tsare wani matashi a gidan yari a jihar Ekiti

- Ana zargin wannan mutum ne da yi wa wata ‘Yar shekara 50 fyade

- Jami’an ‘Yan Sanda sun bada shekarar wannan matashi a Kotu da 29

A jiya ne wata kotun majistare da ke garin Ado Ekiti ta bada umarni a tsare mai shekara 29 a Duniya a gidan kaso da ke babban birnin na jihar Ekiti.

Jaridar Punch ta rahoto cewa ana zargin wannan mutumi mai suna Olaleye Jimoh, da laifin yin lalata da wata Baiwar Allah mai shekaru 50 da haihuwa.

Jami’in ‘yan sanda, Oriyomi Akinwale, ya shaida wa kotu a ranar Alhamis, 28 ga watan Junairu, 2021, cewa ana zargin Mista Olaleye Jimoh da laifin fyade.

Akinwale ya ce an kama matashin ne a ranar 24 ga watan Junairu, 2021, a shiyyar Odo-Owa Ekiti, garin Ikole Ekiti, ana zargin ya aikata laifin ne kafin ranar.

KU KARANTA: Dangote ya yi alkawarin bani N1m duk wata a matsayin toshiyar baki

A cewar jami’in tsaron; “Za a hukunta duk wanda ya aikata irin wannan laifi a karkashin sashe na 358 na dokokin laifuffukan jihar Ekiti na shekarar 2012.”

Rahoton ya bayyana cewa Akinwale ya roki kotu ta ba shi damar ya dauki takardar karar ya kai wa darektan tuhuma domin a dauki matakin da ya kamata.

Olaleye Jimoh ya bayyana a gaban kotu, yayin da ya samu wani lauya mai suna, Busuyi Ayorinde, ya tsaya domin ya ba shi kariya daga zargin da ake yi masa.

Alkali mai shari’a, Adefunmike Anoma ta saurari karar, a karshe ta ce a tsare wanda ake zargin.

KU KARANTA: Ana narka kudi domin tallafawa talakawa amma babu fa'ida – Ndume

Kotu ta bada umarnin a tsare Mai shekara 29 da ake zargi da laifin fyade
Kotun majistare a Legas
Asali: Depositphotos

A ranar 4 ga watan Maris, 2021, mai shari’a Adefunmike Anoma, za ta cigaba da zama domin ta karasa sauraron karar bayan an dakatar da zaman a ranar Alhamis.

A makon nan mu ka ji cewa wani sabon nazari ya nuna amfanin wiwi a jikin Bil Adama wajen takaita illar annobar cutar COVID-19 da ta addabi mutane a Duniya.

Binciken masanan da aka yi a a Kanada ya tabbatar da irin fa’idar wiwi a jikin masu Coronavirus

Jami’o’in Calgary da na Lethbridge da ke kasar Kanada ne su ka gudanar da wannan bincike tare da hadin-gwiwar masu binciken da ake kira Pathway Research Inc.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: