Yanomami: Kabilar da Dangi Ke Bandar Gawar Mamaci, Su Cinye Namansa

Yanomami: Kabilar da Dangi Ke Bandar Gawar Mamaci, Su Cinye Namansa

  • Kabilar Yanomami da ake samu a wasu kasashen kudancin kasar Amurka sun sha banban da sauran kabilun duniya a al'adar mutuwa
  • Sabanin sauran al'adun mutane, Yanomami suna kona gawar mamaci tare da yin bandar namansa kamar dabba
  • Sai dai, kabilar ba haka kawai ta ke yin hakan ba, mabiya kabilar na da wani azanci irin nasu da yasa suke yin hakan

Yanomami ko Yanam wacce wasu ke kira Senema wata Kabila ce mai al'adar ban mamaki ta babbaka gawar mamaci sannan su cinye namansa.

Kabilar, wacce ake samu a kasashen yankin Kudancin Amurka, musamman a Brazil da Venezuela, basa binne mutum kamar yadda aka saba a sauran al'adun kabilun Duniya.

Har ila yau, mutanen kabilar basu damu da amfani da kayan zamani ba, sun kasance masu matukar riko ga al'adunsu na gargajiya.

Kara karanta wannan

Obasanjo, Buhari, IBB Da Lokuta 9 Da Shugaban Najeriya Ya Zama Shugaban ECOWAS

A bisa al'adar kabilar, za'a kare ran mutumin da ya mutu ne ta hanyar gasa namansa a cinye sabanin a binne shi ya rube a cikin turbaya.

Kabilar yanomami da dangi ke bandar gawar mamaci, su cinye namansa
Yanomami: Kabilar da dangi ke bandar gawar mamaci, su cinye namansa. Hoto: The Guardian
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yanomami suna kone gawar dan uwansu tare da yin bandar ta, su cire kasusuwa daga tsoka, rahoton Guardian.

KARANTA: Haba, Malam Sani: Auren dattijo da matashiyar budurwa ya yamutsa hazo

Hatta kasusuwan ba a zubar dasu, ana dakasu, su koma gari wanda ake amfani da shi wajen kada wata miya da suka yarda cewa tana magani.

Bayan sun kone gawar mutum, Yanomami sukan jika tokar gawar, su goga a fuskokinsu kamar fenti sannan su yi waka tare da kuka na nuna alhinin mamacin.

Sai dai, ba kowacce gawa ke samun wannan karramawa ba, misali; idan aka kashe dan kabilar, Mata ne za su kone gawarsa tare da gudanar da sauran al'adun da maza suka saba yi wa mamaci.

Kara karanta wannan

Muje Zuwa: El-Rufai Ya Magantu Kan Yadda Kamun Ludayin Gwamnatin Shugaba Tinubu Ya Kawo Sauyi

A kwanakin baya ne Legit.ng ta rawaito cewa wani mayakin kungiyar Boko Haram da aka kama ya bayyana cewa Shekau ya samu nakasa a kafafunsa, a saboda haka ba ya iya tafiya daidai.

Matashin mayakin mai suna Mohammed Adam, wanda dakarun rundunar soji suka kama, ya ce Shekau ya samu raunuka a wani luguden wuta da sojoji suka yi a sansanin 'yan Boko Haram.

A cewarsa, lamarin ya faru ne a yankin Tumbuktu da ke cikin dajin Sambisa, babbar maboyar kungiyar Boko Haram a jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng