Yan Boko Haram na gangami a jihata, Gwamnan Nasarawa ga Buhari

Yan Boko Haram na gangami a jihata, Gwamnan Nasarawa ga Buhari

- Gwamna Abdulla Suli na Nasarawa ya kai ziyara fadar shugaban kasa ranar Juma'a

- Wannan ya biyo bayan karuwar da ya sama ta yan biyu da amaryarsa ta haifa masa

- Gwamnan ya kawo bukatu biyu wajen shugaba Muhammadu Buhari

Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya kai kuka kan yadda yan ta'addan Boko Haram suka fara gangami a jiharsa suna cin karensu ba babbaka.

Gwamnan yayi jawabi ga manema labaran fadar shugaban kasa bayan zamansa da shugaba Buhari a fadarsa ta Aso Villa, dake birnin tarayya Abuja, rahoton The Nation.

A cewar gwamnan, mambobin kungiyar masu tada kayar bayan Boko Haram, wadanda aka fitittika a hanyar Abuja/Nasarawa a bara sun sake gangami a iyakar da ta raba Nasarawa da Benue suna kai hare-hare.

Ya bayyana cewa makasudin ziyararsa ga Buhari shine kan matsalar tsaron da jihar ta Nasarawa ke ciki da kuma yiwuwan baiwa gwamnatin tarayya titin Jitata Road, wata hanya da ta hada Abuja da Nasarawa.

Ya ce wasu yan Boko Haram da ake kira Darussalam sun gudu da jihar Neja bayan an hallakasu kuma aka kama mutum 900 cikinsu.

Gwamnan ya jaddada cewa wadanda aka damke sunce lallai su yan kungiyar Boko Haram ne.

Sule ya ce jiharsa ta Nasarawa na fuskantar kalubale da dama kuma yana kyautata zaton shugaban kasa zai dau mataki.

DUBA NAN: Kotu ta jefa direba Kurkuku kan kashe N2m da aka tura masa cikin kuskure

Yan Boko Haram na gangami a jihata, Gwamnan Nasarawa ga Buhari
Yan Boko Haram na gangami a jihata, Gwamnan Nasarawa ga Buhari Hoto: @presidency
Asali: Twitter

KU DUBA: Za mu fara yiwa duk mai son shiga Kano gwajin Korona, Ganduje

A bangare guda, Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya tuhumci wasu sarakunan gargajiya a jihar da yiwa gwamnatinsa zagon kasa wajen kokarin kawo karshen matsalar tsaron jihar.

Gwamnan, a wata ganawa da yayi da shugabannin hukumomin tsaro a jihar ranar Alhamis, ya ce sarakunan gargajiya ba sa taka nasu rawan wajen yaki da yan bindiga.

Ya ce hakan ya sa matsalar tsaro ta kara tsanani a jihar kwanakin nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng