Batanci ga Annabi a Kano: Lauyoyi na tsoron taimakawa Yahaya Sharif-Aminu
Lauyoyi masu rajin kare hakkin bil adama dake zaune a jihar Kano sun bayyana tsoronsu kan taimakawa Yahaya Sharrif-Aminu, mawakin da yayi batanci ga manzon Allah (SAW).
Wannan shine dalilin da yasa har yanzu ya gaza daukaka karar hukuncin kisan da kotun shari'ar ta yanke masa ranar 10 ga Agusta, 2020.
Yahaya Sharif-Aminu na da wa'adin kwanaki 30 da zai iya daukaka kara kafin a iya zartar da hukuncin da kotu ta yanke kansa kuma yanzu saura kwanaki goma wa'adin ya kare.
Jaridar Punch ta bayyana cewa wasu lauyoyin kare hakkin bil adama sun bayyana mata cewa lauyoyi da dama na gudun shiga lamarin Yahaya Sharrif saboda tsoron abinda ka iya biyowa baya musamman jiha irin Kano.
Wani dan rajin kare hakkin yace. "Yawancin lauyoyi masu kare hakkin bil adama a Kano da na bukata su shiga lamari suna ki saboda tsoro."
"Yawancinsu na tsoron matasa na iya kona musu ofishohinsu ko a kai musu hari ko kuma a kashesu don suna kare mai batanci."
"Abin mamakin shine, wasu daga cikin lauyoyin nan na goyon bayan hukuncin kisan da akayi masa shiyasa suka ki tabuka komai."
"Kuma sanannan abu ne idan aka zo kan lamuran addini, yan sanda na son kai ko kuma su kawar da kai. Shugabannin addini shiru sukeyi da bakinsu ko kuma su mara goyan baya saboda suna son cigaba da kasancewa kan mulki."
Tuni dai Kungiyar Lauyoyi Musulman Najeriya sun bayyana goyon bayansu ga hukuncin kisan.
A ranar Alhamis, Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje a ranar Alhamis ya ce a shirye ya ke ya saka hannu domin a zartar da hukuncin kisar da kotu ta yanke wa mawaƙi Yahaya Sharif-Aminu da ya yi ɓatanci ga Manzon Allah (SAW).
Da ya ke jawabi bayan taron masu ruwa da tsaki a ranar Alhamis, Ganduje ya ce kotu ta bawa wanda aka yanke wa hukuncin wa'adin kwanaki 30 don ɗaukaka ƙara, idan bai ɗaukaka karar ba shi kuma ba zai bata lokaci wurin rattaba hannu a kan hukuncin ba.
Idan za a iya tunawa babban kotun Shari'a da ke Kano ta samu Aminu-Shariff da laifin batanci kuma ya yanke masa hukumcin kisa ta hanyar rataya.
A watan Maris ɗin shekarar 2020, mawaƙin mai shekaru 22 ya rera wata waƙa mai ɗauke da batanci ga Manzon Allah ya tura a dandalin sada zumunta ta WhatsApp, hakan ya sa mutane suka harzuƙa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng