Dadiro ta sace jaririn matar saurayinta bayan ya kawota gidansu da sunan matar aboki

Dadiro ta sace jaririn matar saurayinta bayan ya kawota gidansu da sunan matar aboki

- Wata budurwa ta ci amanar wani saurayinta da ya ci amanar matarsa ta hanyar gabatar da ita a matsayin matar aboki da za'a koyawa sana'a

- Bayan matar mutumin ta saki jiki da dadiron mijinta, ta ci amanarta, ta gudu da jaririyarta da kuma katinta na ATM da ta aiketa da shi

- Mijin matar ya amsa cewa budurwar masoyiyarsa ce amma bashi da hannu a batun sace jaririyarsu

Mrs Stella Babatunde, Mahaifiyar wata jaririya da aka sace a jihar Ondo, ta bayyanawa manema labarai yadda budurwar mijinta ta sace mata jaririya har gida, kamar yadda Vanguard ta rawaito.

Matar ta ce, tun da fari mijin nata ne ya kawo budurwarsa wurinta da sunan za'a koya mata ɗinkin kaya, ya kuma yi mata ƙaryar cewa matar abokinsa ce amma daga ƙarshe ta gano cewa budurwarsa ce.

A ta bakin matar, ta ce, "Mijina ne ya kawo ta da zummar koya mata sana'ar ɗinkin kaya a ranar 3 ga watan Disambar 2020.

KARANTA: Kaduna: 'Yan bindiga sun kashe jarirai uku a harin da suka kaiwa 'yan tawagar biki

"Ranar Asabar 2 ga Janairu, 2021, matar ta zo shago kamar yadda ta saba. Bayan na yiwa jaririyata wanka da rana sai ta roƙe ni na ba ta jariryar za ta goya ta.

Dadiro ta sace jaririn matar saurayinta bayan ya kawota gidansu da sunan matar aboki
Dadiro ta sace jaririn matar saurayinta bayan ya kawota gidansu da sunan matar aboki
Asali: Getty Images

"Sai na bata ita na kuma hada mata da katin ATM dina don ta ciro min kuɗi ₦3000 da wani abokin ciniki ya turo min ta asusun bankina."

KARANTA: Adadin mutanen da kowacce jiha ta rasa sakamakon ayyukan ta'addanci a 2020

Mahaifiyar jaririyar ta cigaba da cewa; "bayan na ba ta jariryar, ashe guduwa ta yi da ita, na kira mijina a waya don sanar da shi amma ya ƙi dagawa, da ya dawo na nasar da shi sai naga bai nuna damuwarsa ba, lamarin da ya fusatani na kira 'yan sanda."

Bayan da yan sanda suka cafke mijin, ya amince da cewa budurwarsa ce ya kawo wurin matarsa amma bai da masaniya akan sace jaririyarsu.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Ondo, Tee Leo Ikoro, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya kara da cewa suna nan suna bibiyar wacce ake zargin ta sace jaririn.

Legit.ng ta rawaito cewa wata mata yar Najeriya ta sha alwashin matuƙar mijin ta ya nemi da su yi gwajin jinin ƴaƴansu na DNA, to tabbas kamar ya nemi takardar saki ne, kamar yadda The Nation ta rawaito.

Matar mai suna Mrs Eniola Carolina Herrera wacce ta tofa albarkacin bakinta ta shafinta na Tuwita kan batun da ake ta cacar baka a kafafen yaɗa zumunta na zamani, ta sha alwashin rabuwa da mijinta matuƙar ya buƙaci da su yi gwajin DNA.

Ana yin gwajin DNA ne domin tabbatar da hakikanin mahaifin yaro, yarinya, ko yara.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng