Iran shirye take ta taimakawa Najeriya wajen kawo karshen ta'addanci, Jakada

Iran shirye take ta taimakawa Najeriya wajen kawo karshen ta'addanci, Jakada

- An yi bikin zagayowar shekara guda da kisan kwamamdan rundunar Quds na Iran, Qassem Soleimani

- Amurka ta dau alhakin kisan Qassem Soleimani yayinda ya isa kasar Iraqi

- Iran ta bayyana shirin taimakawa Najeriya wajen yaki da yan ta'adda

Jakadan kasar Iran zuwa Najeriya, Ambasada Mohammad Alibak, ya bayyana cewa gwamnatin kasarsa shirye take da taimakawa Najeriya wajen kawo karshen ta'addanci.

Yayinda hirarsa da Nigeria Tribune, ranar Litinin, jami'in diflomasiyyan ya bayyana cewa kasarsa na damuwa kan irin halin tabarbarewan tsaron da ya addabi Najeriya.

Domin kawo karshen haka, ya bayyana cewa "Idan Najeriya ta shirya bamu hadin kai, zamu taimaka wajen kawo karshen ta'addanci a kasar."

Yace: "Jamhurriyar Musulunci ta Iran ta samu kwarewa mai amfani a wannan fanni sakamakon dogon yakin da tayi da ta'addanci."

"Tun daga farkon kungiyar ISIS da gwamnatin Amurka ta kirkira, marigayi Qassem Soleimani, na kan gaba wajen yaki da wannan kungiyar."

"Ka'idar jamhurriyar Iran shine shirye take a koda yaushe domin hada karfi da kasashen da ke fama da matsalar rashin tsaro."

"Sakamakon haka, mun gana sau tari da jami'an gwamnatin Najeriya kuma mun bayyana musu shirye muke da hada kai dasu kan lamuran tsaro."

Alibak ya yi wannan jawaban ne ranar cika shekara daya da mutuwar tsohon kwamandan Sojin Iran, Qassem Soleimani.

KU KARANTA: Ma'aikata sama da 300 ba a biyansu albashi a Majalisar Dokoki

Iran shirye take ta taimakawa Najeriya wajen kawo karshen ta'addanci, Jakada
Iran shirye take ta taimakawa Najeriya wajen kawo karshen ta'addanci, Jakada Credit: Tribune
Asali: Facebook

KU KARANTA: A ranar guda: Mutane 1200 sun kamu da cutar Korona a Litinin

A ranar 3 ga Junairu, 2020, Amurka ta kai mumunan harin jirgin sama domin hallaka babban kwamandan kasar Iran, Qassem Soleimaini da kwamandan rundunar Kata’ib Hezbollah na Iraqi, Abu Mahdi Muhandis.

Hedkwatan hukumar Sojin Amurka, Pentagon, ta tabbatar da hakan a jawabin da ta saki cewa lallai harin Amurka ya kashe kwamandan rundunar Al-Quds na Iran, Qassem Soleimani, a filin jirgin saman Baghdad dake Iraq.

Hedkwatar Sojin Amurkan ta ce shugaban kasa, Donald Trump, ne ya bada umurnin kashe kwamandojin biyu dake shirin kai hari ofishin jakadancin Amurka a Iraqi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel