Buhari da Farfesa Zulum sun gana a fadar shugaban kasa

Buhari da Farfesa Zulum sun gana a fadar shugaban kasa

- Farfesa Babagana Umara Zulum, gwamnan Jihar Borno, ya ziyarci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a fadarsa

- Fadar shugaban kasa da ofishin gwamna Zulum basu fitar da sanarwa dangane da ganawar ba ya zuwa yanzu

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya karbi bakuncin gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, a fadarsa, Villa, wacce ke Aso Rock a birnin tarayya, Abuja.

Hadimin shugaban kasa, Buhari Sallau, ya wallafa hotunan ziyarar da Farfesa Zulum ya kai wa Buhari a fadarsa.

Sai dai, Sallau bai yi karin bayani a kan dalilin ganawar ba. Kazalika, fadar shugaban kasa ko ofsihin gwamna Zulum basu bayyana dalilin ganawar ba ya zuwa yanzu.

A kwanakin baya ne Farfesa Zulum ya ce duk da kisan manoma 43 da mayakan kungiyar Boko Haram su ka yi a Zabarmari, tsaro ya karu a jihar a karkashin mulkin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kamar yadda Punch ta rawaito.

Buhari da Farfesa Zulum sun gana a fadar shugaban kasa
Buhari da Farfesa Zulum sun gana a fadar shugaban kasa @Buharisallau
Asali: Twitter

Farfesa Zulum, ya bayyana hakan ne ranar Lahadi yayin da ya karbi bakuncin kungiyar dattijan arewa a karkashin jagorancin shugabanta, Ambasada Shehu Malami, da kuma sakatarenta, Audu Ogbeh.

Hakan na kunshe ne a cikin jawabin da gwamnatin jihar Borno ta fitar ranar Litinin mai taken 'Zulum: Duk da kashe-kashe, shaidu a kasa sun nuna cewa an fi samun zaman lafiya a karkashin mulkin Buhari a Borno.

A baya Legit.ng ta rawaito cewa majalisar wakilan Najeriya ta fidda sanarwar ƙaryata neman afuwar Shugaba Buhari bisa gayyatarsa ya gurfana gaban majalisar don bayani kan matsalar tsaro da ta addabi ƙasa.

Sanarwar ta ƙaryata rahotannin da wasu kafafen yaɗa labarai ke fitarwa kan cewar ƴan majalisar za su roƙi afuwar Shugaban ƙasa bayan sun amince da ƙudirin gayyatarsa, kamar yadda BBC ta wallafa.

Wasu ƴan majalisa daga jihar Borno ne suka nemi a gayyato shugaba Buhari don ya yi bayani akan halin rashin tsaro da ake fama da shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng