Sheikh Ibrahim Nyass: Diyar shugaban darikar Tijjaniyya ta rasu

Sheikh Ibrahim Nyass: Diyar shugaban darikar Tijjaniyya ta rasu

- Diyar shugaban darikar Tijjaniyya Sheikh Ibrahim Inyass, Sayyada Maryam Sheikh Inyass, ta rasu a kasar Senegal

- Marigayiyar ta kasance mai hidima tare da sadaukar da rayuwarta wajen harkokin da suka shafi addinin Musulunci

Sayyada Maryam Sheikh Ibrahim Inyass, diya wurin shugaban darikar Tijjaniyya, Sheikh Ibrahim Inyass, ta rasu a kasar Senegal kamar yadda Daily Trust ta tabbatar.

Marigayiya Maryam ta kasance mai hidima tare da sadaukar da rayuwarta wajen harkokin da suka shafi addinin Musulunci, lamarin da ya sa ake mata lakabi da 'Hadimar Qur'ani'.

A nan gida Najeriya, annobar cutar korona ta zama sanadiyyar mutuwar tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom a karkashin mulkin soja, Air Commodor Idongesit Nkanga, a ranar Alhamis, kamar yadda NewswireNGR ta rawaito.

KARANTA: Bidiyon Sheikh Karibu Kabara: Ina ajiye da zirin gashin Annabi da aka bani kyauta shekaru 8 da suka gabata

NewswireNGR ta rawaito cewa gidan talabijin na Channels ya wallafa cewa tsohon gwamnan ya rasu yana da shekaru 68 a wani asibiti da ke Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom. Ba'a bayyana sunan asibitin ba.

Sheikh Ibrahim Nyass: Diyar shugaban darikar Tijjaniyya ta rasu
Sheikh Ibrahim Nyass: Diyar shugaban darikar Tijjaniyya ta rasu
Asali: UGC

Marigayi Nkanga ya kasance gwamnan jihar Akwa Ibom daga watan Satumba na shekarar 1990 zuwa watan Janairu na shekarar 1992 a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB).

KARANTA: An wallafa hotunan wasu kayayyaki da Annabi Muhammad ya yi amfani da su

Kafin rasuwarsa, marigayi Nkanga ya na rike da shugabancin kungiyar kishin yankin kudu maso kudu, Neja-Delta (PANDEF).

A ranar Juma'a ne Legit.ng ta rawaito cewa Allah ya yi wa majidadin Kano kuma makaman masarautar karaye, Alhaji Musa Saleh Kwankwaso, rasuwa.

Marigayi Musa Saleh ya kasance mahaifi wurin tsohon gwamnan Kano kuma tsohon sanata, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso

Za'a yi jana'izarsa da misalin karfe uku na ranar Juma'a a unguwar Bompai da ke cikin birnin Kano.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel