Sojoji sun sheke 'yan fashi uku a daura da sansanin NYSC da ke Mangu, sun kwaci bindigu
- Rundunar sojin Operation Safe Heaven ta kashe 'yan fashi da makami 3 a garin Filato
- An halaka su ne a ranar Laraba yayin da suke sintiri a sansanin bautar kasa da ke Mangu
- An kama 'yan fashin ne yayin da suka tarkato wasu kayayyaki da suka hada da wayoyi
Sojojin atisaye na musamman (Operation Safe Heaven), masu wanzar da zaman lafiya sun kashe ƴan fashi uku, kamar yadda kwamandansu, Chukwuemeka Okonkwo, ya faɗi kuma Premium Times ta rawaito.
Mr Okonkwo ya bayyana hakan ne ga kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a ranar Alhamis a garin Jos.
A cewarsa, an sheƙe ɓatagarin ne a daren ranar Laraba lokacin wani sintiri a sansanin masu bautar ƙasa (NYSC) dake Mangu Halle, ƙaramar Hukumar Mangu dake jihar.
KU KARANTA: An kama 'Ahmed Musa' na bogi da laifin damfarar N700,000 a Kano
Ya ce uku daga cikin ƴan fashin sun tsere da raunukan alburushi.
"A daren ranar Laraba ne mazajen mu suka sheƙe ƴan fashi a titin sansanin ƴan bautar ƙasa (NYSC) da ke Mangu."
"Ƴan fashin sun sace kayayyakin da suka haɗa da wayoyi da sauran muhimman abubuwa."
"Bayan sojojin mu sun ɗauki lokaci suna tirzawa da su, an yi nasarar sheƙe uku daga cikin su shida."
"Sauran kuma sun tsere da raunukan harsashi zuwa maƙwabtan ƙauyuka," a cewarsa.
Kwamandan ya ce an ƙwato wasu makamai daga hannunsu wanda suka haɗar da bindigun gargajiya biyu, ƙananun bindigu 5, da sinƙin fakitin alburusai.
Ya ce an miƙa gawarwakin matattun 'yan ta'addadar zuwa Caji Ofis ɗin ƴan sanda dake Mangu.
A wani labari na daban, mai magana da yawun shugaban ƙasa, Femi Adeshina, ya bayyana cewa akwai wata makarkashiya mai kama da juyin mulki da ake shiryawa shugaban ƙasa da cewa wai ba shi ne ke mulkin ƙasar nan ba.
Cikin bayanan nasa, Adeshina ya ce masu kulla wannan makarkashiya na shirin yaɗa wasu labaran ƙarya nan da yan kwanaki masu zuwa, kamar yadda TheCable ta rawaito.
Ya ja hankalin jama'a da su yi watsi da da duk jita-jita da za su kitsa don bata shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Asali: Legit.ng