Karin kudin wuta: An bankado yadda jami'an NERC suka yi watandar biliyoyi

Karin kudin wuta: An bankado yadda jami'an NERC suka yi watandar biliyoyi

- A yayin da 'yan Nigeria ke tsaka da kukan karin kudun wutar lantarki, sai ga shi an bankado badakala a hukumar NERC

- Wani dan kishin kasa ya rubuta takardar korafi zuwa hukumar EFCC tare da sanar da ita yadda manyan jami'ai suka yi watanda da biliyoyi a NERC

- Hukumar NERC ce ke kula da rarraba wutar lantarki da kuma kayyade farashin kudin wuta da 'yan kasa zasu biya

Dai-dai lokacin da yan Najeriya ke korafin ƙarin kuɗin wutar lantarki, sai ga shi ana zargin kwamishina da membobin hukumar rarraba wutar lantarki (NERC) da rabawa kansu biliyoyin Naira a matsayin albashi ta barauniyar hanya.

Gidan jaridar na Premium Times ya samu wata takarda da aka aikewa Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) da wani ɗan kishin Najeriya ya rubutawa kokensa akai.

A cikin takardar korafin, Sam Amadi, ya bayyana wasu kwamishinoni guda bakwai da suka raba Naira miliyan 75 kowannensu wanda adadin ya haura miliyan 525 domin sayan manyan motoci masu tsada kawai.

KARANTA: Rundunar soji ta bayyana dalilin Shekau na yin ikirarin cewa Boko Haram ce ta sace daliban Kankara

Mai korafin, Amadi, ya bayyana rashin gwamsuwarsa na rabawa Kwamishinonin miliyan 75 kowannensu.

Karin kudin wuta: An bankado yadda jami'an NERC suka yi watandar biliyoyi
Karin kudin wuta: An bankado yadda jami'an NERC suka yi watandar biliyoyi @Channels
Asali: Twitter

Bayanai daga wasu majiyar ya nuna an yi amfani da kudin ne don shigo da motocin alfarma daga Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

KARANTA: 2023: An gano dalilin Gwamnonin PDP na juyawa shugaban jam'iyya baya, sun fara neman magajinsa

Takardar korafin ta ce, "Duk motocin an sayo su kuma an yi musu rijista da sunayen wadannan kwamishinoni".

A Cewar rahoton, ya nuna shugaban hukumar ta NERC na karɓar albashi sama da Naira miliyan 83.4 abinda ya saɓa da wanda doka ta sahale masa na miliyan 59.9 kamar yadda kuma hukumar NERC ta yarje.

A kwanakin baya ne Legit.ng Hausa ta rawaito cewa kotun ICC mai tuhumar manyan laifukan ta'addanci da cin zarafin jama'a ta ce za ta binciki hukumomin tsaron Nigeria.

Mai gurfanarwa a kotun ta ce ofishinta ya na kwararan hujjoji na zahiri da za'a iya kimantasu a kan jami'an hukumomin tsaron Nigeria

Fatou Bensouda, mai gurfanarwa da ke shirin barin gado, ta lissafa wasu manyan laifuka da ICC ke zargin jami'an tsaron Nigeria da aikatawa.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng