Fitattun 'yan Najeriya 5 da suka fuskanci ruguntsumin shari'a a 2020
- 'Yan Najeriya sun ga yadda 'yan siyasa da ma'aikatan gwamnati suka sha artabu a kotu shekarar 2020
- Bayan shugaba Muhammadu Buhari ya tsaya tsayin-daka wurin kawar da bata-gari a fannoni daban-daban
- Tun daga matsalolin cin hanci, rashawa, sata, zuwa na kalubalantar nasara a kan wata kujerar siyasa
Jaridar Legit.ng ta bayyana wasu sanannun mutane 5 'yan Najeriya wadanda aka yi ta cece-kuce a kan shari'arsu a 2020.
1. Ibrahim Magu (Shugaban EFCC da aka dakatar)
Antoni janar na gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, ya zargi Magu da almundana da wawusar kudaden al'umma.
Shugaba Buhari har shiga batun yayi, inda ya wakilta Justice Ayo Salami don yayi bincike a kan zargin da ake yi wa tsohon shugaban EFCC din.
Kwamitin binciken ta bukaci shugaban kasa ya fatattaki shugaban EFCC din lokacin da aka gabatar da rahoton.
2. Sanata Dino Melaye (Sanata mai wakiltar Kogi ta yamma)
An sallame shi ne bayan wata shari'a da majalisar tarayya ta kai a kan korafin zabe. Dino Melaye bai samu nasarar komawa majalisa ba, bayan kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Smart Adeyemi.
KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace shugaban ma'aikata, sun halaka direbansa a Edo
3. Abdulrasheed Maina (Tsohon shugaban hukumar fansho)
EFCC ta zargi Maina da satar N2,000,000, 000. An zarge shi da kalmashe N100,000,000,000 na kudden fansho. A ranar Alhamis, 3 ga watan Disamba aka damko Maina a jamhuriyar Nijar, bayan yayi watanni 3 da samun beli, ya fara boye wa.
Sai da Ali Ndume ya tsaya wa Maina, amma ya tsere ya bar shi a gidan gyaran hali. Da kyar kotu ta bayar da belin Ndume a ranar Juma'a 27 ga watan Nuwamba, bayan tabbatar da kyawawan dabi'unsa da nagartarsa.
4. Sanata Orji Uzor Kalu (Tsohon gwamnan jihar Abia)
Kotun koli ta rushe hukuncin da aka yanke wa tsohon gwamnan jihar Abia, na shekaru 12 a gidan gyaran hali saboda zarginsa da rashawa.
A watan Disamban 2019 ne aka yanke masa hukuncin bisa zarginsa da satar kudaden al'umma. A ranar Juma'a, 8 ga watan Mayu, Justice Amina Augie ta yanke masa hukuncin.
KU KARANTA: APC: Za mu tabbatar da cewa abinda ya faru a Kankara bai sake faruwa
5. Olisa Metuh (Tsohon sakataren jam'iyyar PDP na kasa)
Justice Okon Abang na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya yanke masa hukuncin shekaru 7 a gidan gyaran hali bayan kwashe shekaru 4 ana hukunci.
An kama shi da laifin satar dukiyar al'umma, har N400,000,000, kamar yadda EFCC ta tabbatar. An kama shi ne a watan Janairun 2016.
A wani labari na daban, wasu 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kwashe dalibai daga makarantar islamiya a garin Mahuta da ke karamar hukumar Dandume ta jihar Katsina.
Kamar yadda jaridar Katsina Post ta wallafa, an kwashe daliban ne bayan sun kammala maulidi a Unguwar Al-Kasim da ke wani kauye a kusa da su.
Rundunar 'yan sandan jihar Kstina ta ceto dalibai 84 wadanda 'yan bindigan suka sace a garin Mahuta da ke karamar hukumar Dandume, Channels Tv ta wallafa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng