Tsohuwa mai shekaru 81 ta rasu, ta bar wa makwabta gadon N2.8bn

Tsohuwa mai shekaru 81 ta rasu, ta bar wa makwabta gadon N2.8bn

- Renate Wedel ta mutu a watan Disamban 2019 tana da shekaru 81, ga ta da dukiya mai yawa amma babu magaji

- Sakamakon haka gaba daya anguwar Waldsolm, mai dauke da kauyaku 3 suka azurce bayan mutuwarta

- Tsohuwar ta bar dukiya mai dumbin yawa a banki, tsadaddun abubuwa, gidaje da hannayen jari

Wata mata 'yar kasar Jamus, mai suna Renate Wedel, ta mutu a watan Disamban 2019 tana da shekaru 81 a duniya, ta barwa makwabtanta gado mai dumbin yawa. Tun a shekarar 1975 aka yi kiyasin tana da dukiya mai kimar $7,500,000, wanda yayi daidai da N2,861,250,000.

Matar, wacce ta zauna da marigayin mijinta, Alfred Wedel, a Waldsolms, tsakiyar Jamus.

Dama anguwar Waldsolm tana da kauyaku 6 a karkashinta. Bankuna sun yi ta kiran shugaban anguwar, suna sanar dashi batun zunzurutun dukiyar da ta bari.

Mijin Renates ya mutu ne tun 2014, sannan 'yar uwarta ta rasu. Dukiyoyin da ta bari sun hada da gidaje, tsadaddun abubuwa, kudade da kuma hannayen jari, kamar yadda aka ruwaito.

KU KARANTA: Bidiyon Buhari ya ziyarci shanunsa a Daura ya janyo cece-kuce

Tsohuwa mai shekaru 81 ta rasu, ta bar wa makwabta gadon N2.8bn
Tsohuwa mai shekaru 81 ta rasu, ta bar wa makwabta gadon N2.8bn. Hoto daga urbannews254
Asali: Instagram

KU KARANTA: 2023: Magoya bayan Tinubu sun kai ziyarar neman goyon baya fadar babban basarake

Za ka yi tunanin mutanen anguwar za su bukaci zunzurutun kudin, sai dai, wata dabara suka je da ita. Inda suka ce za su yi amfani da kudadenta don a gina abubuwan da al'umma za ta amfana. Sun bukaci gina wuraren wasan yara, wurin wanka da sauran kayan amfanin yara.

A wani labari na daban, wani dan Najeriya mai suna Mustapha Yusuf ya yi tattaki tun daga jihar Sokoto har jihar Bauchi, don nunawa gwamna Bala Mohammed kauna sakamakon nasarorin da ya samu tun bayan hawansa mulki.

Gwamnan ya baiwa Yusuf kyautar mota kirar Peugeot 406 a matsayin kyauta don nuna farin cikinsa.

Mutumin ya yi tattakin ne don ya yabawa gwamnan a kan cigaban da ya samar a jiharsa, inda yake kara masa kwarin guiwa a kan ya cigaba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng