IPMAN ta jihar Kano ta bada sabon farashin litar man fetur

IPMAN ta jihar Kano ta bada sabon farashin litar man fetur

- IPMAN ta yankin jihar Kano ta rage farashin man fetur maimakon N168 kowacce lita zuwa N162.44

- Hakan ya biyo bayan rage N5 a kowacce lita da NNPC tayi ga 'yan kasuwar bayan jin kukan al'ummar Najeriya

- Shugaban IPMAN ya ce za a fara siyar da man a N162.44 daga ranar Litinin, 14 ga watan Disamban 2020

IPMAN ta yankin jihar Kano ta umarci mambobinta da ke karkashin jihar Kano da su koma siyar da fetur N162.44 ko wacce lita daga ranar Litinin.

Gwamnatin tarayya ta rage kudin daga N168 zuwa 162.44 kowacce lita bayan jin kukan jama'a, The Punch ta wallafa.

Shugaban IPMAN na jihar Kano, Alhaji Bashir Dan-Malam ya bayar da wannan umarnin yayin tattaunawa da manema labarai a Kano ranar Litinin.

A cewarsa, hakan ya biyo bayan rage kudin kaya ga 'yan kasuwanni da NNPC tayi, daga N153.17 zuwa N148.17 daga ranar Litinin, 14 ga watan Disamban 2020.

KU KARANTA: Satar 'yan makaranta: Dalibai 668 ne har yanzu babu, Hukumar makaranta

IPMAN ta jihar Kano ta bada sabon farashin litar man fetur
IPMAN ta jihar Kano ta bada sabon farashin litar man fetur. Hoto daga @MobilePunch
Source: Twitter

Ya ce tunda gwamnatin tarayya ta rage N5 ga 'yan kasuwa, don haka babu makawa su rangwanta wa al'umma a gidajen man su.

"Ina umartar mambobin IPMAN na jihar Kano da su fara sayar da mai N162.44 kowacce lita, a bisa umarnin gwamnatin tarayya," a cewarsa.

"Ina so in tabbatar wa da jama'a cewa muna yin iyakar kokarinmu wurin tura kaya duk jihohin da suke karkashin Kano, kamar Katsina, Bauchi, Yobe da Jigawa, musamman a lokutan shagulgula irin wannan don gudun yankewar kayan."

Ya kuma yabawa gwamnatin tarayya bisa sauraron kukan al'umma bisa karin kudin man fetur.

A cewarsa, IPMAN za ta cigaba da baiwa gwamnatin tarayya hadin kai don tabbatar da ko wanne bangare na kasar nan ya samu man fetur.

KU KARANTA: Hotunan sojin Najeriya suna tsaro da taya manoman Zabarmari girbi a gona

A wani labari na daban, kungiyar hadin kan arewa ta ce ta fara tattaki zuwa Daura, garin shugaba Muhammadu Buhari, don zanga-zanga a kan satar daliban GSSS Kankara a jihar Katsina.

Idan ba a manta ba, Shugaba Buhari ya isa garin Daura a ranar Jama'a, ana saura mako daya 'yan bindiga su je makarantar.

Kakakin CNG, Abdul-Azeez Suleiman a ranar Litinin ya tattauana da Punch, inda yace 'yan kungiyarsu za su isa gidan shugaban kasa yau din nan sannan har yanzu ba a ga ragowar daliban ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel