Masari ya ziyarci Daura domin yi wa Buhari jawabi a kan daliban Kankara

Masari ya ziyarci Daura domin yi wa Buhari jawabi a kan daliban Kankara

- Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ziyarci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a Daura

- Bashir Ahmad ya wallafa cewa Masari ya ziyarci Buhari ne domin yi masa jawabi dangane da batun satar dalibai a Kankara

- Tuni wata kungiyar arewa ta sanar da cewa tana tattaki zuwa garin Daura domin fara zaman dirshan a gidan Buhari

A kokarin gwamnati na rubanya kokarinta wajen ceto daliban da aka sace a kamarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara, gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ziyarci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a Daura.

A cewar hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, Masari ya ziyarci Buhari ne domin yi masa bayani a kan inda aka kwana dangane da batun daliban makarantar sakandiren Kankara da 'yan bindiga suka kwashe.

Hedikwatar rundunar tsaro (DHQ) ta baza sojojin kasa da na sama domin nemowa da kuma kubutar da daliban makarantar sakandiren kimiyya ta Kankara, jihar Katsina, da 'yan bindiga suka sace, kamar yadda HumAnge ta rawaito.

HumAngle ta rawaito cewa kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Masari ya ziyarci Daura domin yi wa Buhari jawabi a kan daliban Kankara
Masari ya ziyarci Daura domin yi wa Buhari jawabi a kan daliban Kankara @Bashirahmad
Source: Twitter

A wasu 'yan shekaru da suka gabata ne rundunar sojin sama ta kaddamar da wani sansani na musamman (FOB) a Katsina da kuma wata cibiyar mayar ta martanin gaggawa (QRW) a Daura.

An kafa cibiyoyin ne domin su taka muhimmiyar rawa wajen yakar da 'yan bindiga da sauran miyagun 'yan ta'adda.

Dakarun rundunar sojin sama daga cibiyoyin za su taimaka wajen neman daliban ta hanyar amfani da jiragen sama na musamman masu na'urorin leken asiri.

KARANTA: Ya samu nakasa; mayakin Boko Haram ya fallasa gaskiyar halin Shekau ke ciki

Isah Gambo, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, ya sanar da cewa tuni an fara bincike da bin sahu domin gano dukkan sauran daliban da har yanzu ba'a san inda suke ba tun bayan harin 'yan bindigar.

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa hadakar wasu kungiyoyin arewa sun ce zasu yi tattaki zuwa garin Daura, mahaifar shugaba Buhari, domin gudanar da zanga-zanga a kan sace dalibai akalla 333 a sakandiren kimiyya da ke Kankara, jihar Katsina.

Har yanzu fiye da dalibai 300 ne ake zargin cewa su na hannun 'yan bindigar da suka shiga cikin dakunansu na kwana, a makarantar sakandiren kimiyyya da ke Kankara, su ka yi awon gaba da su.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun dira makarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara, jihar Katsina, da talatainin daren Juma'a zuwa duku-dukun safiyar Asabar, tare da yin awon gaba da dalibai kusan 600.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel