Katsina: Bayan dawowar 200, rundunar 'yan sanda ta bayyana adadin daliban da ke hannun 'yan bindiga

Katsina: Bayan dawowar 200, rundunar 'yan sanda ta bayyana adadin daliban da ke hannun 'yan bindiga

- Rahotanni da sanyin safiyar ranar Asabar sun wallafa labarin yadda 'yan bindiga suka kai hari wata makarantar sakandire a Katsina

- 'Yan bindiga sun dira dakin kwanan dalibai da ke makarantar sakandiren kimiyya a Kankara tare da yin awon gaba da dalibai

- A yayin da rahotanni suka bayyana cewa wasu daga cikin daliban sun dawo, har yanzu da dama sun bace

Har yanzu fiye da dalibai 300 ne ake zargin cewa su na hannun 'yan bindigar da suka shiga cikin dakunansu na kwana, a makarantar sakandiren kimiyyya da ke Kankara, su ka yi awon gaba da su, kamar yadda TheCable ta rawaito.

TheCable ta yi ikirarin cewa majiyar jami'an ta sanar da ita cewa har ya zuwa yammacin ranar Asabar ba'a san makomar dalibai 345 ba, ba'a san inda suke ba.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun dira makarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara, jihar Katsina, da talatainin daren Juma'a zuwa duku-dukun safiyar Asabar, tare da yin awon gaba da dalibai kusan 600.

KARANTA: Bidiyon yadda Maina ya yanke jiki ya fadi a kotu

Rundunar 'yan sanda ta sanar da cewa akwai kimanin dalibai 800 a cikin makarantar, a lokacin da 'yan bindigar suka kai harin, amma wasu daga cikinsu sun samu damar sulalewa ta hanyar tsallaka katangar makaranta.

Katsina: Bayan dawowar 200, rundunar 'yan sanda ta bayyana adadin daliban da ke hannun 'yan bindiga
Katsina: Bayan dawowar 200, rundunar 'yan sanda ta bayyana adadin daliban da ke hannun 'yan bindiga @Vanguard
Asali: Twitter

'Yan bindigar sun harbe wani maigadi da ke kula da tsaron harabar makarantar.

A ranar Asabar ne rundunar 'yan sanda ta sanar da cewa an samu kimanin dalibai 200 da suka dawo daga baya.

KARANTA: Bidiyon Sheikh Karibu Kabara: Ina ajiye da zirin gashin Annabi da aka bani kyauta shekaru 8 da suka gabata

Isah Gambo, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, ya sanar da cewa tuni an fara bincike da bin sahu domin gano dukkan sauran daliban da har yanzu ba'a san inda suke ba tun bayan harin 'yan bindigar.

Legit.ng ta wallafa cewa sakamakon harin da yan bindiga suka kai makarantar, gwamna Aminu Bello Masari, ya bada umurnin kulle dukkan makarantun kwanan jihar Katsina.

Gwamnan ya bada umurnin ne yayin magana da manema labarai bayan ziyarar da ya kai makarantan ranar Asabar.

Masari ya ce a kulle makarantun kuma dalibai su koma gidajensu.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel