Da kafa, magidanci ya taka nisan Abuja zuwa Kano don tserewa matarsa

Da kafa, magidanci ya taka nisan Abuja zuwa Kano don tserewa matarsa

- Forrest Grump magidanci ne dan kasar Italiya wanda aka tsinta a wani yanki mai nisa

- Ya ce bala'in matarsa ne yasa ya tattaka nisan Abuja zuwa Kano a kafa a cikin kasar

- Sai dai 'yan sanda sun zargesa da karya dokar kulle yayin da jama'a suka dinga yi masa jinjina

Wani magidanci dan kasar Italiya mai suna Forrest Grump an tsince shi yana tsaka da tafiya a yankin Adriatic coast da ke kasar Italiya, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Ya bar gidansa da ke Como a makon da ya gabata kafin 'yan sandan da ke Fano su tsare shi.

An zarge shi da karya dokar kullen korona tare da sanya masa haraji. An gano cewa fada yayi da matarsa shine yasa ya fara tattakin.

Bayan an tuhumesa, ya sanar da 'yan sanda cewa ya yi tattakin nisan kilomita 450 daga Como zuwa Fano domin gujewa matarsa.

KU KARANTA: Budurwa ta kamu da korona, an daura aurenta da masoyanta sanye da kayan kariya

Da kafa, magidanci ya taka nisan Abuja zuwa Kano don tserewa matarsa
Da kafa, magidanci ya taka nisan Abuja zuwa Kano don tserewa matarsa. Hoto daga @daily_trust
Source: Twitter

Hakan kuwa yana nufin ya yi tattaki misalin nisan babban birnin tarayya zuwa iyakokin Kano da Jigawa a Najeriya.

Da farko wata mujalla da ke kasar Italiya ta fara wallafawa kuma tuni hakan ya janyo cece-kuce a duniya.

Wasu sun ce kada a ladabtar da shi amma a jinjina masa da yadda yayi kokarin gujewa nada wa matarsa mugun duka.

"Lafiya ta kalau, kawai na gaji kadan," ya sanar da 'yan sanda.

"A kafa na zo, ban yi amfani da wani nau'in sufuri ba."

KU KARANTA: Maryam Sanda: 'Yan sanda sun damke matar auren da ta halaka mijinta

A wani labari na daban, Bai wuce makonni 2 kenan da wata budurwa ta banka wa saurayinta wuta a Festac, jihar Legas ba.

Wata budurwa ta kona nata saurayin a gidansa da ke layin Shaahu da ke karamar hukumar Gboko, a jihar Benue a kan kin aurenta da yayi.

Ganau sun tabbatar da yadda budurwar ta banka wa gidan wuta da misalin 1:30am a ranar Litinin, bayan saurayin mai suna Jude, mahaifiyarsa da wani karamin yaro sun kwanta barci, Vanguard ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel