Kaftin Mukhtar Usman, tsohon shugaban NCAA ya rasu
- Kaftin Mukhtar Usman, tsohon shugaban hukumar NCAA, ya rasu a daren ranar Talata a asibiti
- Ilitrus Ahmadu, shugaban wata kungiyar harkar sufurin jiragen sama, ya tabbatar da rasuwar Kaftin Usman da safiyar ranar Laraba
- An haifi marigayi Kaftin Usman a ranar 5 ga watan Disamba na shekarar 1956
Tsohon babban darekta a hukumar NCAA (Nigerian Civil Aviation Authority), Kaftin Mukhtar Usman, ya rasu, kamar yadda jaridar Punch ta tabbatar a cikin rahoton da ta wallafa.
Kaftin Usman ya rasu a daren ranar Talata a Zaria bayan takaitacciyar rashin lafiya.
Ya rasu ya na da shekaru 63 a duniya.
Punch ta rawaito cewa Ilitrus Ahmadu, shugaban wata kungiyar harkar sufurin jiragen sama, ya tabbatar mata da rasuwar Kaftin Usman da safiyar ranar Laraba.
KARANTA: Ruf-da-ciki a kan tallafin Korona: An dakatar da wasu ma su Sarauta a Kano (sunayensu)
"Yanzu na ke samun labarin mutuwarsa. An garzaya da shi zuwa asibiti a daren jiya (Talata) a Zaria, jihar Kaduna, kafin daga bisani ya ce ga garinku nan," Kamar yadda Ahmadu ya sanar da Punch ta wayar tarho.
An haifi marigayi Kaftin Usman a ranar 5 ga watan Disamba na shekarar 1956.
A shekarar 2014 aka nada shi a matsayin babban darektan hukumar NCAA, inda ya shafe shekaru 5 yana jagoranci, kafin ya mika mulki ga shugaba mai ci, Kaftin Musa Nuhu, bayan karewar zangon mulkinsa a watan Oktoba na shekarar 2019.
KARANTA: An kama Mohammed Usman, kasurgumin dan ta'adda da ya kashe shugaban jam'iyyar APC na jihar Nasarawa
Kafin ya zama babban darektan NCAA, Kaftin Usman ya taba rike mukamin kwamishina a hukumar binciken hatsarin jirgin sama.
Kazalika, ya taba rike mukamin manajan darekta a tsohon kamfanin sufurin jiragen sama na Najeriya.
A wani labarin, Legit.ng Hausa ta rawaito cewa wasu ɓatagari sun harbi DPO ofishin ƴan sanda da ke Otukpo, SP Yahaya Pawa da safiyar ranar Talata a unguwar Otukpo da ke Makurdi, babban birnin jihar Benue.
Jaridar Daily Trust ta gano cewa DPO Pawa ya jagoranci tawagar jami'an ƴan sandan don su ƙwamuso wasu masu laifi da ake zargin sun fake a yankin da lamarin ya afku.
An gano cewa masu laifin suna da hannu dumu dumu a satar kayayyakin da akayi a kasuwar Otukpo lokacin da gobara ta tashi a makon dsa ya gabata.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng