Yadda soja mace ta dinga zabga wa gurgu mari a kan ya tsawatar wa yaron ta

Yadda soja mace ta dinga zabga wa gurgu mari a kan ya tsawatar wa yaron ta

- Wata soja ta ci zarafin wani gurgu saboda ya dakatar da danta daga tsallaka titi shi daya

- Kamar yadda mutumin yace, yana hanyar kai yaransa makaranta al'amarin ya faru

- Ya ce matar ta janyo shi daga cikin mota ta hau dukan shi kamar Allah ya aikota, a gaban yaran shi

Wani gurgu ya zargi wata soja da cutar dashi saboda ya kwaba wa danta a wuraren Mokola a Ibadan, jihar Oyo.

Bidiyon wata soja mai suna Mamman H, ma'aikaciyar barikin Letmuck, tana wanka wa Abolade mari, yayi ta yawo a kafafen sada zumunta.

Abolade ya dakatar da yaron Mamman, mai shekaru 4 da haihuwa a ranar Laraba saboda ya yi yunkurin tsallaka titi shi daya.

Abolade, wanda yake rike da sandar guragu ya sanar da Punch cewa a ranar Alhamis, Mamman da wasu mutane sun wulakanta shi, kuma sun yi masa dukan tsiya saboda ya kwaba wa yaron.

Yadda soja mace ta dinga zabga wa gurgu mari a kan ya tawatar wa dan ta
Yadda soja mace ta dinga zabga wa gurgu mari a kan ya tawatar wa dan ta. Hoto daga @MobilePunch
Source: Twitter

KU KARANTA: 'Yan daba dauke da makamai sun kashe matashi bayan ya ci cacar N15m

Kamar yadda yace, "A ranar Laraba, ina hanyar kai yarana makaranta, sai na ga wani yaro yana kokarin tsallake wani babban titi. Sai nayi gaggawar tsayawa, na tambayi ina mahaifiyar yaron take, kowa yayi shiru. Wani mutum yace ya san mahaifiyarsa, amma ba a ganta ba. Sai na ja kunnen yaron, nace kada ya kuskura ya kara tsallaka titi da kan shi.

"Yau da safe (Alhamis) wuraren karfe 7:30am, ina hanyar kai yarana makaranta, wata soja da wasu mutane 5 suka ja abin hawana. Ina isa gefe, matar ta janyo ni daga cikin mota, suka hau dukana. Suna dukana, ina ihu ina neman taimako, bayan mutane sun taru, suka ceceni daga hannunsu. Daga nan ne na iya kai yarana makaranta."

"Ina hanyar dawowa, a lokacin ta sanya kayan sojoji. Tana ganina ta fara dukana, na umarci diya ta da ta fara dauka a waya. Sauran mutanen da suka zo za su fara dukana, suna ganin tana dauka a waya suka janyeta daga wurin," a cewarsa.

KU KARANTA: Rikicin kudancin Kaduna ya dade yana faruwa, Sheikh Gumi

A wani labari na daban, wani Smart Odojie Ofagba, wanda 'yan sanda suka yi sanadiyyar kisan mahaifinsa, Samuel Udojie Ofagba, kawunsa, Abulimen Ofgba da leburan mahaifinsa, Kinsley, yana bukatar gwamnatin tarayya ta biya shi naira miliyan 50.

Ya sanar da wannan bukatar tashi ne yayin sanar da kwamitin bincike a kan wadanda jami'an SARS suka cutar da sauran makamantan laifuka, inda yace wani DPO ne ya kashe masa 'yan uwa a ranar 9 ga watan Maris ta 1999, DPO din shine Aisabor da ke karamar hukumar Usenu Irrua a jihar.

A cewarsa, 'yan sanda sun kama leburan mahaifinsa, bayan ya dawo daga birniya da daddare. Sai suka kai shi wurin mahaifinsa ko zai gane shi, Daily Trust ta tabbatar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel