'Yan daba dauke da makamai sun kashe matashi bayan ya ci cacar N15m

'Yan daba dauke da makamai sun kashe matashi bayan ya ci cacar N15m

- Wasu samari 3 sun sharba wa wani saurayi wuka, inda hakan ya yi ajalinsa

- Ana zargin sun kashe shi ne saboda naira miliyan 15 na cacar da suka yi

- Samarin 3 sun bishi har shagonsa da ke kasuwar Ogbe-Ijoh, inda suka kashe shi

Kamar yadda rahotonni suka kammala, wadanda suka yi aika-aikan sun tsere da wayarsa, bayan sun sara saurayin wuri-wuri a jikinsa. Ya mutu ne ana hanyar kai shi asibiti.

Kawun mamacin, Thomas Ogisi, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar, inda yace mamacin ya yi caca ana saura mako daya a kashe shi, wanda yake sa ran zai samu naira miliyan 15 idan ya samu nasara.

Babu tabbacin an kashe shi ne saboda naira miliyan 15 din, tunda har yanzu ba a samu damar sanin halin da asusun bankinsa yake ciki ba, tunda 'yan ta'addan sun tsere da wayarsa.

'Yan daba dauke da makamai sun kashe matashi bayan ya ci cacar N15m
'Yan daba dauke da makamai sun kashe matashi bayan ya ci cacar N15m. Hoto daga @Thenation
Source: UGC

KU KARANTA: Najeriya ta mallaki dukkan abubuwan da za su iya kawo mata daukaka, Osinbajo

"Yaron yana zaune ne da yayata. A ranar da al'amarin ya faru, sun je kasuwar Ogbe-Ijoh suna shirin komawa gida sai ga wasu maza 3, inda suka dakatar da shi a bakin shagonsa, suka sharba masa wuka.

"Al'amarin ya faru ne da misalin karfe 6pm na ranar Laraba. Bayan sun sara masa wukar suka kwace wayarsa suka tsere. Ya mutu kafin a isa asibiti da shi," kamar yadda Ogisi ya sanar da Daily Independent.

Kamar yadda aka samu labari daga wurin abokansa, an kashe shi ne saboda naira miliyan 15 na caca. Yana jirin ranar Laraba tayi, yadda za a biya shi kudin, sai aka kashe shi ranar Litinin. Wasu daga cikin abokansa sun san batun kudin.

KU KARANTA: Olabisi Ajala: Cikakken tarihin dan Najeriya da ya zagaye kasashe 87 a babur

"Muna bukatar a yi mana adalci a kan kisan wulakancin da aka yi wa dan mu. Mun sanar da 'yan sanda abinda ake ciki, amma bama jin dadin rashin tsaron da ke kasuwa," a cewarsa.

A wani labari na daban, wata budurwa mai suna Jumoke ta sha caccaka a kafar sada zumuntar zamani, bayan ta rabu da saurayinta wanda suka yi shekaru 2 suna soyayya.

Kamar yadda wani Sheyi ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, saurayin budurwar, Femi, ya tambayi budurwar dalilinta na daina kula shi daga nan ne ta nuna masa cewa ta canja sheka.

Jumoke ta fara da ce masa ita fa ta gaji da jiransa, tana bukatar more rayuwarta, ta rike masa amanarsa tun lokacin da suka fara soyayya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel