Saboda kokarin Buhari, yan Boko Haram sun daina karban haraji hannun mutane

Saboda kokarin Buhari, yan Boko Haram sun daina karban haraji hannun mutane

Ministan labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya ce al'ummar Arewa maso gabashin Najeriya sun daina biyan yan Boko Haram haraji.

Yayin magana a ganawarsa da kungiyar masu kamfanonin jarida a Najeria NPAN a Legas ranar Alhamis, Lai Mohammed yace kwace garuruwan da yan Boko Haram ke yi ya zo karshe.

Amma ikirarin Ministan ya ci karo da rahotannin kwana-kwanan nan dake nuna mazauna Arewa maso gabas da Arewa maso yamma na biyan yan bindiga haraji kafin su samu shiga gonakinsu noma.

An ruwaito cewa manoman da aka kashe a Borno karshen makon da ya gabata sun ki biyan harajin ne.

Shi kuwa MInista Lai Mohammed ya ce yan bindigan sun daina haka saboda irin namijin kokarin da shugaba Muhammadu Buhari keyi.

"Kafin hawan shugaban kasa mulki, Boko Haram na iya shiga ko wani gari, musamman a Arewa, su kai hare-hare," Yace

"Birnin tarayya Abuja, Kano, Maiduguri, Jos, da Damaturu ne aka kai hari sosai."

"Har tashohin mota, Coci-coci, Masallatai, da kasuwanni basu bari ba. Amma a yau, abin ya zama tarihi. Yan kunar bakin wani na ci karnukansu ba babbaka suna kashe mutane."

"Amma yanzu ba haka bane. Abubuwa sun canza yau."

"A baya Boko Haram na kwace gari, tsige sarakunan gargajiya da kuma karban haraji. Amma yanzu ba haka bane. Wannan canjin ba wai kawai ya faru bane. nasarorin Sojoji ne karkashin wannan shugaban kasan."

Saboda kokarin Buhari, yan Boko Haram sun daina karban haraji hannun mutane
Saboda kokarin Buhari, yan Boko Haram sun daina karban haraji hannun mutane Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Asali: Legit.ng

Online view pixel