Da duminsa: 'Yan bindiga sun halaka manoma 7, sun sace mutum 30 a Katsina

Da duminsa: 'Yan bindiga sun halaka manoma 7, sun sace mutum 30 a Katsina

- Labaran mutane 43 da 'yan Boko Haram suka yi wa yankan rago a jihar Borno, sun karade ko ina

- Kwatsam sai ga labarin manoma 7 da 'yan bindiga suka yi wa kwatankwacin hakan a Katsina

- Bayan nan, suka sace mutane 30 'yan kauyaku 3 da ke karkashin karamar hukumar Sabuwa

Manoma suna fuskantar rashin tsaro da kisan wulakanci a arewacin Najeriya. Don yanzu ba a garkuwa da mutane kadai 'yan ta'adda suka tsaya ba, har da kisa.

Daily Sun ta ruwaito yadda 'yan bindiga suka yanka manoma 7, ciki har da wata mata mai shayarwa a cikin kauyaku 3, Tashar Bama, Dogun Muazu da Unguwar Maigayya da ke karamar hukumar Sabuwa a jihar Katsina cikin kwanakin karshen mako.

Dan majalisa mai wakiltar mazabar, Hon. Ibrahim Danjuma Machika, ya tabbatar da aukuwar lamarin a majalisar jihar a ranar Litinin, 30 ga watan Nuwamba.

Da duminsa: 'Yan bindiga sun halaka manoma 7, sun sace mutum 30 a Katsina
Da duminsa: 'Yan bindiga sun halaka manoma 7, sun sace mutum 30 a Katsina. Hoto daga www.today.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Abinda yasa rikicin APC na cikin gida yake ci gaba da kamari, DG na PGF

Baya ga kisan da suka yi, sun sace sauran 'yan kauyakun guda 30. Hakan ya faru ne bayan labaran kisan mutane 43 da 'yan ta'addan da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka yi a Zabarmari da ke jihar Borno.

KU KARANTA: Al-Mustapha Abacha ya fallasa shirin wasu shugabanni na tarwatsa Najeriya

A wani labari na daban, ministan Labarai da al'adu, Lai Mohammed, a ranar Litinin yace a yanzu haka an bar Najeriya da 'yan ta'adda saboda an hana ta makaman yakar 'yan ta'adda duk da kokarin da takeyi wurin yakarsu.

Ministan ya nuna alhininsa a kan kisan manoma 43 na Zabarmari, karamar hukumar Jere da ke jihar Borno, inda yace gwamnatin tarayya ba za ta zauna ba har sai ta kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Alhaji Mohammed ya yi maganar ne a Makurdi yayin da ya kaiwa gwamna Samuel Ortom ziyara, inda yace 'yan ta'addan suna samun kudade daga kasashen ketare, Vanguard ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel