Mutum 1 ya sheka lahira yayin arangamar 'yan sanda da 'yan fashin teku
- 'Yan sandan jihar Rivers sun samu nasarar damkar wani dan ta'adda tare da yaransa
- Mutumin ya addabi fasinjojin jiragen ruwan bakin kogin Bonny, da ke Port Harcourt
- Sakamakon harin da suka kai ranar Alhamis, sun ji wa fasinjoji raunuka har da kashe wani
Wani dan ta'adda wanda ya addabi fasinjojin jiragen ruwan kogin Bonny da ke Port Harcourt a jihar Rivers, Dan Ezekiel George, ya shiga hannun 'yan sanda, tare da yaransa bayan sun kai wa wasu fasinjoji hari, har wani mutum ya rasa ransa.
Wanda ake zargin, mai shekaru 28 dan asalin Asarama ne da ke karamar hukumar Andoni a jihar Rivers. 'Yan ta'addan sun yi awon gaba da kayan matafiyan a ranar Alhamis da safe, The Punch ta ruwaito.
Wani mutum, wanda ya nemi a boye sunansa, ya tabbatar wa da manema labarai cewa fasinjoji da dama sun samu mugayen raunuka sakamakon adduna da wukaken da 'yan daban suka yi amfani da su, har wani ya rasa ransa.
KU KARANTA: Maza ne suka tarwatsa rayuwata, mahaifiyar 'ya'ya 4 daga maza daban-daban
Bayan tuntubar kakakin hukumar 'yan sandan yankin, Nnamdi Omoni, ya ce wasu sun zo hannu, amma har yanzu suna farautar wani gawurtaccen 'dan ta'adda.
Omoni ya ce, "Zan iya tabbatar da aukuwar lamarin, don ya faru ne a kogin Bonny. Daniel Clifford George daga Asarama da ke karamar hukumar Andoni, yana daya daga cikin wadanda 'yan sanda suke nema ruwa a jallo. Kuma sun samu nasarar damkarsa tare da abokan tarayyarsa."
Ya tabbatar da cewa Daniel ne shugaban 'yan ta'addan, kuma yanzu haka sun fara tambayarsa don binciko sauran 'yan ta'addan.
KU KARANTA: Dakarun soji sun tarwatsa sansanin 'yan bindiga a iyakar Kaduna da Niger
A wani labari na daban, kakakin rundunar soji, John Enenche, ya sanar da hakan a ranar Alhamis yayin taron bayar da bayani a kan ayyukan rundunar soji.
A cewarsa, ta yadda sojoji suke ragargazar 'yan ta'adda, kwanan nan za su zama tarihi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng