Kasar Saudi Arabia ta magantu a kan kisan manoma 40 a Borno

Kasar Saudi Arabia ta magantu a kan kisan manoma 40 a Borno

- Kasar Saudiyya ta bayyana alhininta a kan kisan manoman jihar Borno da ake zargin 'yan Boko Haram sun yi

- Saudiyya ta mika sakon ta'aziyyarta ga iyalan wadanda al'amarin ya shafa da gwamnatin Najeriya gaba daya

- Ta kuma yi fatan Ubangiji ya nuna ranar da za a kawo karshen ta'addanci da kashe-kashe a Najeriya

Saudiyya ta nuna alhininta a kan kisan manoman shinkafa da ake zargin 'yan Boko Haram sun yi a Borno.

Saudiyya ta wallafa wannan sakon a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, inda ta nuna alhininta a kan yadda maharan suke kai wa fararen hula wadanda ba su ji ba, ba su gani ba fargaba.

Kamar yadda ta wallafa, "Muna mika sakon ta'aziyyarmu ga iyalan wadanda aka kashe, da mutanen jihar, gwamnati da al'ummar Najeriya gaba daya."

KU KARANTA: Sifetan dan sanda ya yi budurwa fyade, yana barazanar kashe kan shi idan ba a yafe masa ba

Kasar Saudi Arabia ta magantu a kan kisan manoma 40 a Borno
Kasar Saudi Arabia ta magantu a kan kisan manoma 40 a Borno. Hoto daga @BBCHausa
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kisan Zabarmari: Ka sallami shugabannin tsaro, NAS ga Buhari

Kasar Bahrain ta mika kwatankwacin ta'aziyyar nan ga Najeriya, inda tace tana fatan ganin karshen ta'addanci a Najeriya nan kusa.

A wani labari na daban, ministan Labarai da al'adu, Lai Mohammed, a ranar Litinin yace a yanzu haka an bar Najeriya da 'yan ta'adda saboda an hana ta makaman yakar 'yan ta'adda duk da kokarin da takeyi wurin yakarsu.

Ministan ya nuna alhininsa a kan kisan manoma 43 na Zabarmari, karamar hukumar Jere da ke jihar Borno, inda yace gwamnatin tarayya ba za ta zauna ba har sai ta kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Alhaji Mohammed ya yi maganar ne a Makurdi yayin da ya kaiwa gwamna Samuel Ortom ziyara, inda yace 'yan ta'addan suna samun kudade daga kasashen ketare, Vanguard ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel