Ganduje ya yi muhimman nade-nade guda hudu a gwamnatin Kano

Ganduje ya yi muhimman nade-nade guda hudu a gwamnatin Kano

- Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi muhimman nade - nade a gwamnatin jihar Kano

- Daga cikin nade-naden da Ganduje ya yi akwai nadin shugaban makarantar CARS da SRCOE

- Ganduje ya bukaci mutanen da aka nada da su yi aiki tukuru wajen sauke nayin da aka dora a kansu

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa Dr Yusuf Musa a matsayin Provost ɗin makarantar share fagen shiga jami'a(CARS).

Ganduje ya kuma naɗa Saminu Bello a matsayin Rejistara Kwalejin Ilmi ta Sa'adatu Rimi (SRCOE).

Acewar babban sakataren yaɗa labarai (CPS), Gwamna Ganduje ya naɗa Garba Baƙo Gezawa a matsayin magatakarda (Clerk) na majalisar jihar Kano.

KARANTA: An cire kwamandan bataliyar sojojin da ke Zabarmari bayan kisan manoma 43

Dukkan naɗe naɗe sun fara aiki nan take.

"Dole ku yi aiki tukuru domin samun nasara da cigaban Jihar Kano. Amfani da fasahar zamani ya zama tilas a al'amurran da suka shafi hukuma a yau", Ganduje ya gayawa sabbin waɗanda ya naɗa.

Ganduje ya yi muhiman nade-nade guda hudu a gwamnatin Kano
Ganduje ya yi muhiman nade-nade guda hudu a gwamnatin Kano @Daily_nigerian
Source: Twitter

"Saboda haka, ku yi aiki tuƙuru da dabarun fasahar bayanai na zamani, kamar yadda ake yi a duniya" a cewarsa.

KARANTA: Sheikh Daurawa ya bayyana yadda makusanta Buhari ke wulakanta Malamai tare da hanasu ganinsa

Ya kuma shawarcesu akan su haɗe kansu, su zama tsintsiya, inda ya tuna musu cewa; "haɗin kai da aiki da juna na kaiwa ga cimma babbar Nasara".

A makon da ya gabata ne Legit.ng Hausa ta rawaito cewa gwamna Ganduje ya bada umarnin a sauya wa gidan gidan Zoo matsuguni daga cikin birni saboda matsarsa da jama'a suka yi.

Kwamishinan Al'adu da harkokin buɗe ido, Ibrahim Ahmad, shine ya bayyana hakan a ranar Laraba, inda ya ce dabbobin, yanzu, a takure su ke a matsunguninsu saboda ko kadan basa son hayaniyar mutane.

Da yake magana da gidan Rediyon Freedom, kwamishinan ya ce za'a sauya matsugin dabbobin zuwa garin Tiga da ke yankin ƙaramar hukumar Bebeji ta jihar Kano.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel