Tsohon mai mulki ya koma tura amalanke, ya sanar da banbancin mulkin yanzu da wancan zamani

Tsohon mai mulki ya koma tura amalanke, ya sanar da banbancin mulkin yanzu da wancan zamani

- Wani tsohon mutum wanda aka gan shi yana tura amalanke na abincin dabbobinsa ya ce tsohon kansila ne shi

- Anibaba ya ce a lokacin mulkin Babangida, N500 ne albashinsa duk da N444 suke tafiya dashi saboda haraji

- Ya ce albashinsu ba shi da yawa a lokacin, amma kuma ayyukan da suke yi suna da matukar yawa

Wani mutum mai suna Anibaba, ya bayyana yadda ya rike kujerar kansila a jihar Legas lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida.

Anibaba ya ce ya rike kujerar kansila a jihar Legas, inda aka ganshi yana tura amalanke da abincin shanu a ciki.

A cewarsa, albashinsa lokacin yana kansila N500 ne, amma ana cire haraji, inda yake tafiya gida da N444 a matsayin albashinsa.

KU KARANTA: Kalamai masu ratsa zuciya da Bashir Ahmad yayi ga matarsa ranar zagayowar haihuwarta

Tsohon mai mulki ya koma tura amalanke, ya sanar da banbancin mulkin yanzu da wancan zamani
Tsohon mai mulki ya koma tura amalanke, ya sanar da banbancin mulkin yanzu da wancan zamani. Hoto daga Kogbagidi
Source: Instagram

KU KARANTA: Gwamnonin arewa maso gabas sun bukaci a basu damar gurfanar da 'yan ta'adda

Ya ce a lokacinsu ne aka kirkiri karamar hukumar Eti-Osa. Gabadaya Ajah tana da kansila daya tal ne, sannan Obalende mazaba guda daya ce.

Ba wannan bane dan siyasa na farko da ya fara bayyana banbanci tsakanin mulkin wannan zamanin da na da ba.

A wani labari na daban, Sophia Koji, wata mata 'yar kasar Ghana mai shekaru 31, ta bayyana yadda tayi ta yaudarar kanta, tayi tunanin maza za su iya kula da ita.

Kamar yadda matar ta bayyana a Crimecheckfoundation.org, tana da yara 4 wadanda ta haifa da maza daban-daban.

Maimakon mazan su kula da ita da yaran, sai suka bar ta tana fama da wahalhalun rayuwa. Sophia ta bayyana yadda ta koma kwana a shago, ita da yaranta sannan suka yi ta fama da yunwa da kishi saboda ta rasa kudaden shiga.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel