Ana bukatanku a filin daga, ba akan 'Black Friday' ba, Shehu Sani ya caccaki Hisbah a Kano

Ana bukatanku a filin daga, ba akan 'Black Friday' ba, Shehu Sani ya caccaki Hisbah a Kano

- Hukumar Hisbah ta Kano na cigaba da shan suka daga bangarori daban-daban

- Bayan sabanin da ta samu da malaman Kano, Sanata Shehi Sani ya yi martani

Tsohon Sanata da ya wakilci mazabar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya caccaki hukumar Hisbah ta jihar Kano kan gargadin da ta yiwa gidan rediyo na amfani da kalman 'Black Friday.'

Sanaya a shafinsa na Tuwita ya ce wannan rashin aikin yi ne kuma yayi kira ga Hisbah ta mayar da hankalinta kan garkuwa da mutane da kashe-kashen da ake yi a Arewa.

"Ranar Juma'a babbar rana ce ga Musulmai. Dan an ambaceta da wani kala ba wani abu bane. Barazabar Hisbah kan amfani da kalmar 'Black Friday' aikin banza ne," cewar Shehu Sani.

"Su mayar da hankali kan kashe-kashe da sace-sacen mutane a garinsu. Ana bukatansu a filin daga," ya kara.

Ana bukatanku a filin daga, ba akan 'Black Friday' ba, Shehu Sani ya caccaki Hisbah a Kano
Ana bukatanku a filin daga, ba akan 'Black Friday' ba, Shehu Sani ya caccaki Hisbah a Kano Hoto: @ShehuSani
Source: Twitter

KU KARANTA: Ku bamu mako daya domin ganin yiwuwar rage farashin mai, gwamnatin tarayya ga kwadago

A bangare guda, fatawar majalisar malaman Kano ta sha ban-ban da na hukumar Hisbah kan lamarin ranar Black Friday da aka haramta fadinsa a jihar Kano don wasu dalilai.

Yayinda Hisbah take ganin Juma'a babbar rana ce kuma bai kamata a alakanta ta da wani abun aibi ba ko yaya ne, majalisar malamai na da ra'ayin babu laifi.

Shugaban majalisar malamai, Malam Ibrahim Khalil, ya bayyanawa tashar rediyo, Freedom, cewa babu laifi cikin bikin ranar 'Black Friday'.

"Tun asali amfani da kalmar 'Black Friday' ba ya nufin mummunan abu, hasalima yabo ne," cewar Malam Khalil.

"Ba magana ce ta suka ba, in ka kalli tarihi, sai dai in mutum bai bincike abin da fadi ba."

Malamin ya kara da cewa bai san dalilin hukumar Hisbah na daukar matakin hana amfani da kalman da tayi ba, kuma idan da sunan addini ne to babu gabar kamawa.

DUBA NAN: Sojoji sun yi artabu da yan bindiga hanyar Abuja/ Kaduna

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel