Harkar tsaro ta tabarbare a Najeriya, in ji Afenifere

Harkar tsaro ta tabarbare a Najeriya, in ji Afenifere

- Kungiyar Yarabawa ta Afenifere ta koka kan tarbarbarewar tsaro a sasan Najeriya

- Kungiyar ta yi wannan jawabin ne yayin martani kan kisar basarake Olufon na Ifon, Isreal Adeusi da 'yan bindiga suka kashe

- Kungiyar ta ce lokaci ya yi da Shugaba Muhammadu Buhari zai dage damtse don tabbatar da tsaro a kasar

Wata ƙungiyar ƙabilar Yarabawa a ranar Juma'a ta nuna damuwarta akan kashe Olufon na Ifon a jihar Ondo, Oba Israel Adeusi wanda wasu ƴan bindiga da har yanzu ba'a gano su ba suka aikata.

Sun bayyana kisan nashi a matsayin kashe da yawa, inda sukayi kiran ga rundunar ƴan sanda kan ta zaƙulo makasan kamar yadda jaridar Tribune ta ruwaito.

Afenire ,tace kisan Olufon ya zo musu lokacin da basa gama farfaɗowa daga kisan ƴar shugaban ƙungiyar ba, Mrs Funke Olakunrin.

Harkar tsaro ta tabarbare a Najeriya, in ji Afenifere
Harkar tsaro ta tabarbare a Najeriya, in ji Afenifere. Hoto daga @TribuneNg
Asali: Twitter

Wadda ake tuhumar wasu makiyaya da aikata kisan, baya ga sauran kashe kashe da har yanzu ƴansanda suka gaza warwaresu.

Lokaci ya yi da shugaban ƙasa Muhammad Buhari zai miƙe tsaye ya tsare Najeriya ya kawo tsarin tarayya da zai inganta tsaron cikin gida.

DUBA WANNAN: 'Yansanda sun yi ram da wata mata mai bawa ƴanfashi, ɓarayi da masu laifi mafaka

Afenire ta bayyana hakan a wani bayani da ta fitar mai taken" kisan Olufon da rashin tsaro" ta hannun Sakatarenta na ƙasa Mr Yinka Odumakin.

Sun ƙara bayyana cewa Afenire ta zo wuya da yawan kashe ƴan ƙasa da ake yi a faɗin ƙasar.

Afenire ta jajantawa iyalan Olufan,da mutanen garin Ifon,Jihar Ondo,da al-ummar Yoruba bakiɗaya.

Ƙungiyar tayi tir da Allah-wadai da afkuwar lamarin.

Afenire lokacin da take kiran ƴansanda kan lamarin ta bayyana kisan nasa a matsayin gazawa da rashin iya aikin jam'an tsaron Najeriya wajen kare rayuka da dukiyar al'umma.

"Kisan gillar yazo muna tsakiyar jimamin kashe ƴar shugaban Afenifere, Mrs Funke Olakunrin, wadda ake tuhumar wasu makiyaya".

"Akwai kashe kashe da ake a ƙasashen yarabawa wanda ƴan sanda suka gaza daƙile su."

"Abin har ya kai jallin ana kashe manyan mutane masu daraja ga muhimmanci ga al'umma da cigabanta wanda ke nuna rashin tsaro a ƙasa."

KU KARANTA: An dawowa da Nigeria gunkin Ife Terracotta mai shekaru 600 daga kasar Netherlands

"Kashe kowanne ɗan ƙasa yana damunmu,musamman na kashe Sarki mai daraja ta ɗaya."

"Muna kira ga ƴansanda su zaƙulo makasan Olufon,wanda yana ɗaya daga cikin kisan da ke nuna gazawa da rashin sanin makamar aiki na jami'an Najeriya."

"Kun kasa tsare rayuka da dukiyarmu a Najeriya,wanda shine haƙƙi na farko da ya rataya a wuyan kowacce irin gwamnati da tasan ciwon al-ummarta.

"Mun gaji da irin kisan da ake yiwa mutane a faɗin Najeriya a kullum"

"Najeriya ta bawa rashin tsaro gurbin zama wanda hakan ke ƙara ta'azzara al'amura a ƙasa"

"Zuwa ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari,lokaci ya yi da zaka miƙe tsaye don inganta tsaron cikin gida".

"Bazai yi wu ka zama shugaban ƙasa mai juya ƙasa ba tare da aiki," acewar Afenifere.

A wani labarin daban, kungiyar gwamnonin Arewa maso gabas, NEFG, ta koka kan abinda ta kira rashin adalci da gwamnatin tarayya ke mata a bangaren gine-ginen tituna a yankin ta.

Kungiyar wadda ta hada da gwamnonin jihohin Adamawa, Bauchi, Borno Gombe, Taraba da Yobe ta bayyana hakan ne a ranar Juma'a cikin sakon bayan taro mai dauke da sa hannun shugabanta, Gwamna Babagana Zulum a karshen taronta na 3 da aka yi a Yola babban birnin Jihar Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng