Hotuna da tarihin yara 3 bakar fata masu matukar kaifin basira a duniya

Hotuna da tarihin yara 3 bakar fata masu matukar kaifin basira a duniya

- Ubangiji yana bayar da kaifin kwakwalwa ga wanda yaso, sannan ya hana wanda yaso

- A rubutun nan za ku ji labari yara 3 wadanda duk duniya sun fi kowa kaifin kwakwalwa

- Yaran suna da matukar azanci da fasaha mai ban al'ajabi da kuma yanayin kwakwalwarsu

Akwai yara masu kaifin kwakwalwa da basira a fadin duniya. Akwai wasu yara bakaken fata da aka gano sunansu Ramarni Wilfred, Anala Beevers da Alannah George a matsayin yara wadanda suka fi duk kowa a kaifin kwakwalwa a duniya.

Yaran 'yan Mensa ne, wacce har yanzu ba a sake samun wadanda suka fi 'yan yankin kwakwalwa ba.

1. Ramarni Wilfred

Ramarni yana da kaifin kwakwalwa 162, fiye da na Albert Einst da Stephen Hawking. Yaron mai shekaru 16 ya fi Bill Gates kaifin kwakwalwa. Tun yana da shekaru 10 da haihuwa yayi rubutu a kan falsafar gaskiya, kamar yadda Face 2 Face Africa suka ruwaito.

Hotuna da tarihin yara 3 bakar fata masu matukar kaifin basira a duniya
Hotuna da tarihin yara 3 bakar fata masu matukar kaifin basira a duniya. Hoto daga africanleadership.co.uk
Source: UGC

KU KARANTA: Buni ga Sanatocin APC: Ku zage damtse, nasara tamu ce a kodayaushe

2. Anala Beevers

Tun Anala tana da shekaru 4 take da kaifin kwakwalwa 145. Tun tana da watanni 10 da haihuwa take iya gane haruffa. A 2014, ta cika shekaru 5, tana iya lissafo sunayen jihohin arewacin Amurka da manyan biranensu idan tana kallon taswira.

Hotuna da tarihin yara 3 bakar fata masu matukar kaifin basira a duniya
Hotuna da tarihin yara 3 bakar fata masu matukar kaifin basira a duniya. Hoto daga face2faceafrica.com
Source: UGC

KU KARANTA: Kin tozarta kan ki a gida da ketare, Jaruma Adesua ta caccaki hadimar Buhari

3. Alannah George

Alannah tana da kaifin kwakwalwa 140, kuma ita ce mafi kankanta cikin 'yan Mensa daga Amurka. Yarinyar ta koya wa kanta karatu tun kafin ta fara zuwa makaranta. Sannan ta iya wake-wake irin na kananan yara 'yan makaranta.

Hotuna da tarihin yara 3 bakar fata masu matukar kaifin basira a duniya
Hotuna da tarihin yara 3 bakar fata masu matukar kaifin basira a duniya. Hoto daga www.un.org
Source: UGC

A wani labari na daban, Hajiya Bisola Rahama Zakariyya, shugabar Elkanemi College of Islamic Theology da ke Maiduguri, ta rasu tana tsaka da gabatar da jawabi, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Al'amarin ya faru ne a ranar Asabar, 21 ga watan Nuwamba. Matar tana sanye da hijabi da takunkumin fuska, tana tsaka da gabatar da jawabi sai ta rasa inda kanta yake, take a nan baki masu saurin tunani suka yi gaggawar zuwa gareta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel