'Yan boko su tashi su karbi mulki kafin mayunwatan matasa su kashe mu
- 'Yar gwagwarmaya, Aisha Yesufu, ta ce al'amura za su cigaba da tabarbarewa a kasa matukar jama'a basu fahimci siyasa ba
- A cewar ta, dole jama'a su ke zaben 'yan takara ma su nagarta ba tare da la'akari da banbancin kabila ko addini ba
- Kazalika, ta shawarci 'yan Boko su tashi tsaye domin jagorantar juyin juya hali ba tare da zubar da jini ba
Aisha Yesufu a wata hira da akayi da ita, ta ce akwai buƙatar ƴan Najeriya masu ilimi su yi amfani da basirarsu don juyin juya hali ba tare da zubda jini ba.
Ta bayyana hakan ne yayin wata hira da tayi da GRACE EDEMA, inda ta bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta sha aikita ta'addanci akan ƴaƴanta, ƴan ƙasa.
"Maganar gaskiya ita ce halayyar gwamnatin Najeriya abin tirr da Allah-wadai ne gami da ɗimautarwa.
"Abin baƙin ciki shine halin ko in kula da gwamnatin Najeriya ke nunawa ƴan ƙasar.
"Gwamnatin rashin gaskiya da rashin kishin ƙasa. Gwamnatin dake cike da masu son rai da zuciyarsu don buƙatarsu ta kansu.
KARANTA: Sunayensu: Dangote ya shigar da karar wasu ma'aikatansa guda takwas
"Ina tunanin abu mafi muhimmanci da zai faru, shine ƴan Najeriya su tuhumi gwamnatinsu.
"Ƴan Najeriya su daina zargin waɗanda abin ya shafa, kamata ya yi su zargi masu tozarcin da cin zarafinsu, kuma a wannan ƙadamin da ake ciki gwamnati ce uwar cin zarafin.
"Dole ne mu tabbatar da cewa ba mu cigaba da bawa gwamnati damar tozarta mu ba da yin abubuwa marasa kyau.
Abu mafi muhimmanci shine ƴan Najeriya su sani ce wa, siyasa itace komai; mutanen da kuka zaɓa su zasu ƙayyade makomar nagartar mulki da gwamnatin da zaku samu.
"Zai yi matuƙar ma'ana idan ƴan Najeriya suka fahimci cewa dole suna buƙatar su zaɓi waɗanda zasu saurari kokensu, masu karsashi, hali na gari, tausayi, sanin ya kamata, da kishin al'ummarsu.
KARANTA: El-Rufa'i ya fadi rukunin 'yan arewa da ke adawa da sauya tsarin mulkin kasa
"Babu tunani da hankali ku cigaba da ɗora mutane bisa addini ko al'ada muddin basu cancanta ba ko kuma bisa tsoron jam'iyyu biyu ne kawai zasu kai labari, wannan ba itace hanyar tafiya ba.
"Idan muka cigaba da zaɓar shafaffu da mai, za su yi tunanin cewar ba zai zama dolensu su cika muradan al-ummarsu ba; tunaninsu zai zamana cewa iya waɗanda suka tsayar da su takara, iyayen gidansu da sauransu su kaɗai zasu cikawa muradansu.
"Ya na da matuƙar muhimmanci ga ƴan Najeriya su fara tabbatar da cewa sune waɗanda suke zaɓo zaƙaƙuran da zasu shige musu gaba don wakiltarsu, saboda idan aka zaɓi nagari, zasu gina tsarin da ya kamaci al-ummarsu.
"Muna buƙatar jajurtacciyar al-umma. Abun da muke da shi a yanzu shine jajurtattun maza da mata amma ba jajurtacciyar al'umma ba.
"Za mu cimma samun jajurtacciyar al-umma ne kaɗai idan muka zaɓi mutanen da suka dace, masu kishi, masu buƙatar abu mai kyawu da nagarta ga ƙasarmu Najeriya ba wai kansu ba.
"Wadanda suka damu da makomar kasa ba wai zaɓen gaba ba.
"Idan muka sami irin waɗannan mutanen ne kaɗai a matsayiin wakilan mu zamu kai ga nasara da samun tsarin da zai cikawa mabuƙata muradansu tare da tabbatar da kowa ya samu kulawar da ta dace," a cewarta.
A ranar Talata ne Legit.ng ta wallafa cewa Gidan jaridar BBC ma su yada labarai sun fitar da jadawalin mata masu a fada a ji na duniya na shekarar 2020 inda sunan Aisha Yesufu ya samu shiga.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng