zargin wawure ₦400m: ICPC ta yi ram da Farfesan ilimin ƙananan kwayoyin halittu bisa

zargin wawure ₦400m: ICPC ta yi ram da Farfesan ilimin ƙananan kwayoyin halittu bisa

- Hukumar yaƙi da zamba da almundahana da laifukan da suka danganci hakan (ICPC) ta cakume Farfesa zugudum

- Farfesan, wanda ya kasance masani a bangaren ilimin kananan kwayoyin halituu, shine mukaddashin shugaban cibiyar NABDA

- ICPC ta na zarginsa da barna tare da yin watanda da kudin cibiyar NABDA ta nazari da bunkasa fasahar kimiyyar halittu

Babban daraktan wucin gadi na cibiyar nazari da bunƙasa fasahar kimiyyar halittu (NABDA) kuma Farfesan ilimin ƙananan kwayoyin halittu da fasahar kimiyyar halittu ya shiga hannu.

Hukumar yaƙi da zamba da almundahana da laifukan da suka danganci hakan (ICPC) ce ta kama Farfesan bisa zarginsa da sama da faɗi da zunzurutun kuɗaɗe har Naira miliyan ɗari hudu (₦400m).

Bincikenn sirri na hukumar ICPC ya nuna cewa daraktan wucin gadin ya sauya akalar kuɗaɗen hukumar zuwa ajihuhunan wasu jama'a.

DUBA WANNAN: El-Rufa'i ya bayyana rukunin 'yan arewa da ke adawa da gyara da sauye - sauye a salon mulki

Farfesan ya wawura tare da raba kuɗaɗen tare da wasu manyan ƙusoshin hukumar.

Wannan dalilin ne yasa jami'an hukumar ICPC suka yi ram da shi don ya amsa tambayoyin tuhuma akan yadda kuɗaɗen sukayi ɓatan dabo da saninsa.

zargin wawure ₦400m: ICPC ta yi ram da Farfesan ilimin ƙananan kwayoyin halittu bisa
zargin wawure ₦400m: ICPC ta yi ram da Farfesan ilimin ƙananan kwayoyin halittu bisa
Asali: UGC

Daraktan wucin gadin yana fuskantar tuhuma bisa tuggun da ya ƙulla da cin mutuncin ofishinsa.

DUBA WANNAN: DHQ ta kaddamar da manhajar AFNDSP domin sojoji da iyalansu

Laifinsa ya saɓa da doka kuma akwai hukuncinsa a ƙarƙashin sashe na 19 da na 26 na kundin laifuffukan rashawa, zamba, da almundahana da sauran madangantan laifuka na shekarar 2000.

Ana cigaba da gudanar da bincike kan daraktann wucin gadin, inda hukumar ICPC ta bayyana cewa zata ɗauki matakin da ya dace a kan Farfesan da zarar an kammala bincike.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel