IG na yan sanda ya karawa kananan jami'ai 82,779 girma

IG na yan sanda ya karawa kananan jami'ai 82,779 girma

Sifeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu, ya karawa kananan jami'an hukumar 82,779 matsayi zuwa na gaba.

A jawabin da Kakakin hukumar, Frank Mba, ya saki ranar Litinin, ya ce yan sandan sun hada da Sajen 56,779, Kofura 17,569 da Konstable 8,431.

A cewarsa, an yi wannan karin matsayin ne domin karawa yan sandan karbin gwiwa saboda su kara kaimi a aiki, Channels ta ruwaito.

"Sifeto Janar na yan sanda, IGP M.A Adamu, mni, a yau, 23 ga Nuwamba 2020 ya amince da kara girman kananan yan sanda dubu tamanin da biyu, dadari bakwai da saba'in da tara (82,779), " wani sashen jawabin yace.

"Karin matsayin ya hada daSajen 56,779 zuwa Sifeto, Kofura 17, 569, da Konstabu 8,431 zuwa Kofira."

Hakazalika, an baiwa matattun yan sanda 16 karin matsayi na musamman yayinda aka yiwa wasu raunatattun yan sanda 70 karin matsayi saboda raunukan da suka samu yayin zanga-zangar ENDSars.

IG na yan sanda ya karawa kananan jami'ai 82,779 girma
IG na yan sanda ya karawa kananan jami'ai 82,779 girma Hoto: The Nigerian Police
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Online view pixel