Yadda matasa suka bawa barawo lemo don ya samu karfi su sake jibgarsa

Yadda matasa suka bawa barawo lemo don ya samu karfi su sake jibgarsa

- Wasu matasa da suka kama barawo sun taimake shi da abin sha mai zaki domin kawai ya samu karfi su kara jibarsa

- Matasan sun kama matashin dumu-dumu da laifn sata a Takoradi da ke kasar Ghana

- Bayan barawon ya fita daga hayyacinsa saboda duka, matasan da ke dukansa sun bashi lemo don ya farfado su sake yi masa rubdugu a karo na biyu

Rahotanni sun nuna yadda wasu matasan ƙasar Ghana suka taimaki wani mutum ta hanyar dawo masa da kuzarinsa saboda su jibge shi a karo na biyu bisa zarginsa da aikata halin ɓera.

Acewar rahotanni, wasu matasa a Takorodi ta kasar Ghana sun bawa wani ɓarawo abin sha mai ƙara ƙarfi da kuzari, bayan ya galabaita, kawai don ya dawo hayyacinsa su ƙara dukansa a karo na biyu.

DUBA WANNAN: Zaria: 'Yan bindiga sun kai farmaki rukunin gidajen lakcarorin ABU, sun yi awon gaba da Farfesa

Wani ganau ba jiyau ba wanda ya watsa labarin, ya ce an kama ɓarawon dumu dumu da laifin sata.

Yadda matasa suka bawa barawo lemo don ya samu karfi su sake jibgarsa
Yadda matasa suka bawa barawo lemo don ya samu karfi su sake jibgarsa @Vanguard
Asali: Twitter

Maimakon miƙa shi ga hukuma ko rundunar ƴansanda, sai matasan unguwar suka ɗauki doka a hannunsu, suka yi masa dukan kawo wuƙa.

Bayan sun fahimci ya galabaita kuma dukan ya daina shiga jikinsa, sai sukayi sauri suka bashi abin sha mai ƙara kuzari da ƙarfi na "Rush" don ya dawo hayyacinsa su ɗora daga inda suka tsaya.

DUBA WANNAN: Ganau: Yadda shugaban APC na jihar Nasarawa ya yi ta ihun 'a taimaka min' kafin a kashe shi

Wannan ganau shine ya yaɗa hoton lokacin da matasan suka zagaye ɓarawon yana tsaka da shan lamurjen ƙarin kuzarin.

Anyi rubutu a jikin hoton kamar haka; "barka da zuwa Takoradi, kasar Ghana, gurin da aka zane wani ɓarawo, sannan mu ka bashi abin sha mai sinadarin ƙarin kuzari na Caffeine saboda kawai mu ƙara jibgarsa.Wannan shine irin karamcinmu. Babu inda ya kai Takoradi".

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa, sabbin batutuwa sun ɓullo kan yadda aka kashe, Philip Schekwo, shugaban jam'iyyar APC na jihar Nasarawa da ƴan bindiga suka sace shi, sannan suka kashe shi.

Majiyoyi sun bayyana cewa masheƙan sun zo gidan Schekwo da ke kan titin Kurikyo kusa da cocin Dunamis da ke Bukan Sidi a garin Lafia da misalin ƙarfe sha ɗaya na dare 11pm inda suka fara harbi kan mai uwa da wabi.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng