A shirye muke da mu saurari matasanmu, Gwamnonin arewa

A shirye muke da mu saurari matasanmu, Gwamnonin arewa

- Gwamnonin jihohin arewa sun ce a shirye suke da su saurari matasan arewa

- Shugaban gwamnonin, Simon Lalong ne ya fadi hakan a wani taro da suka yi a Kaduna

- Gwamnan jihar Filaton ya ce wajibi ne sauraron matasa don neman cigaba

Gwamnonin jihohin arewa sun ce a shirye suke da su saurari matasan yankin a kan matsalolin da suke fuskanta.

Shugaban kungiyar gwamnonin arewa, Simon Lalong, ya fadi hakan a ranar Laraba a Kaduna yayin taron rantsarwar kwamitin matasa, wacce aka kirkira musamman don samar da mafita ga yankin.

A wata takarda da jami'in hulda da jama'ar gwamnan, Macham Makut ya saki, ya ce wajibi ne samar da ayyukan yi, kawar da jahilci, ta'addanci da talauci ga matasa ta hanyar kirkirar kwamiti.

A cewarsa, an kirkiri kwamitin, wacce Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Bamalli yake jagoranta, sakamakon taron da masu ruwa da tsakin arewa suka yi, The Punch ta wallafa.

KU KARANTA: Yadda yaro mai shekaru 18 ke farfasa bangon gidansu idan an hana shi abinci

A cewar Lalong, "Matasa sun fi kowa yawa a kasar nan, don haka su ne masu ruwa da tsaki a kasar nan.

"Wajibi ne a sauraresu, kuma a yi amfani da shawarwarinsu don tafiyar da mulki yadda ya kamata.

"Wajibi ne a matsayinmu na shugabanni mu janyo matasa a jikinmu, don sanin matsalolinsu."

Sarkin Zazzau ya tabbatar da cewa kwamitin za ta tabbatar da cewa ta dage wurin tallafawa da taimaka wa matasa.

A shirye muke da mu saurari matasanmu, Gwamnonin arewa
A shirye muke da mu saurari matasanmu, Gwamnonin arewa. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Matashi ya yi wa budurwa mugun duka tare da yunkurin kasheta a kan kudin da ya kashe mata a fitarsu ta farko

A wani labari na daban, wani bidiyo ya yi ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani, na wani ma'aikacin ofishin jakadancin Najeriya na kasar Jamus, wanda aka gan shi yana tattauna yadda zai hadu da wata mata a otal yayi lalata da ita don yayi gaggawar samar mata da fasfoti.

A wata takarda ta ranar Talata, ofishin jakadancin sun dakatar da shi don su tabbatar da gaskiyar zargin da ake yi masa na lalata da sauran laifuka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel