Yadda yaro mai shekaru 18 ke farfasa bangon gidansu idan an hana shi abinci

Yadda yaro mai shekaru 18 ke farfasa bangon gidansu idan an hana shi abinci

- Ina tsoron ya rasa ransa saboda mugun ci, baya saurarawa abinci, cewar wata mata a kan danta

- Matar ta ce yaronta yana kwasar gara ya ci kamar Allah ya aiko shi, shiyasa ya zama jibgege

- Har tsakar dare yake tashi ya ci iya cinsa, idan ta hana shi abinci yayi ta fasa bangon gidanta

Wata mata mai suna Katie Price, ta bayyana yadda take boye abinci don dakatar da jibgegen danta daga mugun ci.

A cewarta, har tsakar dare yake tashi yayi ta kwasar abinci yana ci, shiyasa yayi tulele, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Matar mai shekaru 42 ta bayyana yadda babban danta yake bubbula mata bangon dakuna idan ta hana shi cin abinci.

Harvey, mai shekaru 18 yana fama da wata cuta, wacce take sa shi yayi ta kwasar gara kamar Allah ya aiko shi.

Likitoci sun dade suna gargadinsa, da ya rage cin abinci saboda kada ya kamu da ciwon zuciya.

Duk da dagewarta a kansa, amma baya saurara wa abinci. Ta ce kodayaushe cikin yin fulastar bangon gidanta take yi, amma abin ya ci tura.

Ta ce ya san dadin abinci sosai, wani zubin, idan ta bashi dankalin hausa, maimakon na turawa, sai yayi ta kunci. Tana tsoron ya mutu saboda bala'in kwasar gara.

KU KARANTA: Hotunan budurwar da tsohon kwamishinan dan sanda ya fizge wa kunne da cizo

Yadda yaro mai shekaru 18 ke farfasa bangon gidansu idan an hana shi abinci
Yadda yaro mai shekaru 18 ke farfasa bangon gidansu idan an hana shi abinci. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Lalata da masu neman fasfoti: Ofishin jakadancin Najeriya a Jamus ya dakatar da ma'aikaci

A wani labari na daban, ana zargin wani mutum dan Atlanta da yi wa budurwarsa da suka hadu a wata kafar sada zumunta dukan tsiya, bayan sun hadu ido da ido, shafin Linda ikeji.

Ana zargin ya daki budurwar ne, saboda ta zabi abubuwa masu tsada, shiyasa ya daki kudinsa. Benjamin Francher ya shirya haduwa da Brittany Correri a daren Laraba, 11 ga watan Nuwamba.

A ranar haduwarsu ta farko, ya mutunta 'yan uwanta da iyayenta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel