Matasa sun yi caa kan budurwar da tace duk saurayin da bashi da N25m, kada yayi soyayya
- Kafar sada zumuntar zamani ta dauki zafi bayan wata budurwa ta wallafa wata gurguwar shawara
- A cewar budurwar, kada wani saurayin da ya san bashi da a kalla naira miliyan 25 a asusunsa ya kuskura ya fara soyayya
- Budurwar ta sha caccaka, inda samari da 'yan mata da dama suka yi ta tofa albarkacin bakinsu
Kowa yana da ra'ayi da zabi idan aka zo batun soyayya, amma yawancin mutane su kan duba aljihu.
Wata budurwa, mai suna Rutie, ta janyo cece-kuce a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, bayan ta bai wa matasa shawara a kan soyayya.
Kamar yadda Rutie ta ce, duk saurayin da bashi da a kalla naira miliyan 25 a asusunsa, bai dace da soyayya ba.
Nan da nan samari da 'yan mata suka yi ta tururuwa suna yin tsokaci a karkashin wallafar.
Wani Papi Deezy, cewa yayi, "Babu matsala, matukar budurwar tana da a kalla rabin kudin, a nata asusun."
Abiodun ya yi tsokaci da, "Me budurwar ita kuma za ta mallaka kafin a fara soyayyar, kuma ai babu laifi idan mace ta dage wurin neman na kanta ko da babu wani namiji da zai taimaka mata."
KU KARANTA: Hotunan motocin alfarma da Regina Daniels take hawa tun bayan aurenta da Ned Nwoko
KU KARANTA: 2023: Lokacin mulkin Ibo ya yi, Okorocha ya bayyana burinsa na shugabancin kasa
A wani labari na daban, wata 'yar Najeriya, mai suna Chisara Agoha, ta bayyana yadda ta umarci mijinta da ya mallaka mata filinsa, a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.
Ta ce ta aiwatar da hakan ne, inda ta sa ya canja sunan mallakar filin, zuwa nata. Inda tace masa matsawar yana so aurensu ya dore, to yayi gaggawar mallaka mata filin nan.
Kowa yasan yadda mazan Afirika suke katantane dukiyoyin matansu, shine ta gwada yin hakan a kan mijinta, ta gwada ya ya zai ji.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng