Bidiyon Emmanuella tana bayanin yadda ta samu kudin gina wa mahaifiyarta katafaren gida

Bidiyon Emmanuella tana bayanin yadda ta samu kudin gina wa mahaifiyarta katafaren gida

- Emmanuella Samuel, yarinyar nan mai bidiyon ban dariya ta shayar da mutane mamaki bayan ta gina wa mahaifiyarta gida

- Karamar yarinyar, ta bayyana wa duniya yadda ta samu damar tara makudan kudade duk da tana da kananun shekaru

- Ta ce tana raba kudaden da take samu gida 4, kashi daya ta kai gidan marayu, daya gini, dayan iyayenta sai ta adana dayan kason

Yarinyar mai shekaru 10 da haihuwa, ta bai wa mutane mamaki ta yadda ta gina wa mahaifiyarta gida. Sai da Emmanuella ta cika gidan da kayan alatu, sannan ta bai wa mahaifiyar kyautar gidan, kuma ta yi mata alkawarin mayar da ita wani katafaren gida.

A wata tattauanawa da BBC suka yi da ita, ta ce ta so siya wa mahaifinta mota, sai kawunta Mark, ya tuna mata da alkawarin gidan da tayi wa mahaifiyarta. Mark ya shawarceta da ta fara siyan gidan tukunna.

KU KARANTA: Gwamnan Kogi ya ziyarci Buhari, ya mika wata muhimmiyar bukatar jiharsa gabansa

Emmanuella ta yi wa manajanta magana, inda tace ya dinga raba kudaden da take samu gida 4. Tace kashi daya za ta dinga kaiwa gidan marayu, daya kuma gini, wani kason kuma na iyayenta sai kason na karshe ta dinga adanawa.

Bidiyon Emmanuella tana bayanin yadda ta samu kudin gina wa mahaifiyarta katafaren gida
Bidiyon Emmanuella tana bayanin yadda ta samu kudin gina wa mahaifiyarta katafaren gida. Hoto daga @Officialemmanuella
Asali: Instagram

KU KARANTA: 2023: Lokacin mulkin Ibo ya yi, Okorocha ya bayyana burinsa na shugabancin kasa

A cewarta, ta yi kusan shekara 1 tana ginin, tun watan Disamban 2019 ta fara. Tayi matukar farin cikin ganin yadda iyayenta suka shiga matsanancin farinciki, musamman yadda mahaifiyarta tayi ta farinciki. Tace mahaifiyarta ta cancanci gidan da yafi haka. Kuma tana nan da burin siya wa mahaifinta mota.

Jaridar Legit.ng ta yi hira da uncle Mark, inda yace yarinyar diyar makwabciyarsa ce, ya dauketa ne bayan ya ga yana bukatar karamar yarinya don su dinga bidiyon ban dariya tare. Kuma tun da ya dauketa yake samun nasara.

A wani labari na daban, Regina Daniels tana daya daga cikin manyan jaruman Nollywood kuma sanannu, tana da a kalla mutane miliyan 8 da suke bibiyar shafukanta na kafafen sada zumuntar zamani, kamar Instagram.

Kama daga sanda ta fara harkar fim, har zuwa aurenta da mashahurin biloniyan nan kuma sananne, Ned Nwoko, da haihuwar santalelen jaririnta, Munir, mutane su na ta bibiyar rayuwarta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel