Mallake kadarorin miji da matar aure ta bayyana ta yi, ya janyo cece-kuce

Mallake kadarorin miji da matar aure ta bayyana ta yi, ya janyo cece-kuce

- Wata mata mai suna Chisara Agoha, ta bayyana yadda ta tabbatar da soyayyar da mijinta yake yi mata

- A cewarta, sai da ta tabbatar mijinta ya mallaka mata filinsa kwara daya da ya mallaka

- Chisara ta ce babu dalilin da zai sa namiji mai aure ya mallaki wasu kayayyakin kadarori

Wata 'yar Najeriya, mai suna Chisara Agoha, ta bayyana yadda ta umarci mijinta da ya mallaka mata filinsa, a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.

Ta ce ta aiwatar da hakan ne, inda ta sa ya canja sunan mallakar filin, zuwa nata. Inda tace masa matsawar yana so aurensu ya dore, to yayi gaggawar mallaka mata filin nan.

Kowa yasan yadda mazan Afirika suke katantane dukiyoyin matansu, shine ta gwada yin hakan a kan mijinta, ta gwada ya ya zai ji.

Kamar yadda Chisara tace, bayan sun yi aure, ta tashe shi da daddare, inda tace masa tunda sun yi aure, ya mayar da sunan da suke takardar filinsa zuwa nata, tunda yanzu ita ce shugabar gidan.

Wannan wallafar ta Chisara ta janyo cece-kuce a kafar sada zumuntar, inda wasu suke caccakarta, wasu kuma suna yaba mata.

KU KARANTA: Gwamnonin kudu-kudu sun bukaci ban hakuri daga fadar shugaban kasa a kan soke taronsu

Dukkan dukiyar namiji kamata yayi ta zama mallakin matarsa bayan aure, Matar aure
Dukkan dukiyar namiji kamata yayi ta zama mallakin matarsa bayan aure, Matar aure. Hoto daga @Chisara14
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hotunan dan Najeriya da ya garzaya kasar waje ya yi wuff da zukekiyar budurwa sun janyo cece-kuce

A wani labari na daban, wata budurwa wacce take dauke da cikin saurayinta, tana cikin tashin hankali, bayan mahaifiyar saurayin ta ce ba za ta taba barin ta ta auri danta ba saboda bata da kyau.

Budurwar, mai shekaru 28 da haihuwa, duk da ba ta so a bayyana sunanta ba, ta bai wa Arike Ade Pheonix labarin damuwarta don neman shawarar jama'a.

Kamar yadda tace, har saurayin na ta ya kai baiko gidansu, jaridar The Nation ta wallafa. Sai dai, mahaifiyar saurayin ta ce ba za ta amince a yi auren ba saboda nisa da kuma munin budurwar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng