Hotunan budurwar da tsohon kwamishinan dan sanda ya fizge wa kunne da cizo
- Wani tsohon kwamishinan 'yan sanda ya ciji kunnen Faith, mai shekaru 18, har sai da kunnenta ya cire
- Al'amarin ya faru ne bayan wani rikici ya barke tsakanin iyalan mutumin da mahaifiyarta
- Yanzu haka, masu rajin kare hakkin bil'adama suna ta fafutukar kwatar wa Faith hakkinta
Masu rajin kare hakkin bil'adama suna bukatar a yi wa Faith Aigbe, 'yar shekara 18, adalci, wacce wani Ogunbor, kwamishinan 'yan sanda mai murabus, ya cije wa kunne har ya cire.
Al'amarin ya faru ne a layin Eweka, kusa da layin Aduwawa, cikin birnin Benin jihar Edo, a ranar Lahadi, 15 ga watan Nuwamba, bayan rikici ya barke tsakanin mahaifiyar yarinyar da iyalan Ogunbor.
Kamar yadda bayanai suka kammala, yarinyar ta dawo daga coci, sai ta ga matar Ogunbor, diyarsa, da wasu iyalansa suna cutar da mahaifiyarta.
Faith ta ce, daga zuwan Ogunbor, sai ya dauki cebur zai maka wa mahaifiyarta, take a nan tayi gaggawar rike makamin.
Tsohon dan sandan bai yi kasa a guiwa ba ya damki Faith, inda ya dankara wa kunnenta na dama cizo har sai da ya cire, Linda Ikeji ta wallafa.
Kamar yadda rahotonni suka bayyana, Faith da mahaifiyarta sun tafi ofishin 'yan sanda don kai kararsa, amma su na isa, Ogunbor ya tsoratar da su, inda yace shi tsohon kwamishinan 'yan sanda ne.
Ana zargin dan Ogunbor da yaransa da sace mahaifin Faith, inda su ka kai shi wani wuri su ka yi masa dukan tsiya, har sai da 'yan sa kai suka ceceshi.
KU KARANTA: Gwamnonin kudu-kudu sun bukaci ban hakuri daga fadar shugaban kasa a kan soke taronsu
KU KARANTA: Gwamnan Kogi ya ziyarci Buhari, ya mika wata muhimmiyar bukatar jiharsa gabansa
A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Imo, kuma sanata mai wakiltar yankin Imo ta yamma, Rochas Okorocha, ya nuna kwadayinsa a kan tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023, shafin Linda Ikeji ya wallafa.
Tsohon gwamnan, wanda yayi maganar yayin da wata kungiya wacce ta kira kanta da sunan 'Igbos for Rochas 2023 President', wato kungiya mai marawa Rochas bayan shugabancin kasa a 2023, wacce Jeff Nwaoha ya jagoranta, daga jihohi 5 na yankin kudu maso gabas, tace lokacin da kabilar Ibo za ta samar da shugaban kasar Najeriya yayi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng