Gwamnonin kudu-kudu sun bukaci ban hakuri daga fadar shugaban kasa a kan soke taronsu
- Ya kamata fadar shugaban kasa ta fito fili ta ba mu hakuri, cewar gwamnonin kudu-kudu
- Sun sanar da hakan ne sakamakon fasa wani taro da aka yi, bayan sun dade su na jiran a fara
- Rayukansu sun baci, har su na cewa, hakan kamar wulakanci, tozarci da kuma ci musu fuska ne
Gwamnonin kudu-kudu sun bukaci fadar shugaban kasa ta ba su hakuri bayan ta fasa yin wani taron masu ruwa da tsaki da ya kamata a yi a Port Harcourt, Channels TV ta wallafa.
Kamar yadda wata takarda tazo daga gwamnatin jihar Rivers, gwamnatin tarayya ta shirya wani taron gwamnoni a ranar Talata, da sauran shugabannin yankin don tattauna matsalolin da kasa take fama da su, ciki har da matsalar zanga-zangar EndSARS.
Taron ya kunshi har ministocin da shugabannin gargajiyar yankin.
Bayan an canja lokacin yin taron, daga karfe 11am zuwa 1pm, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari, ya sanar da shugaban gwamnoni kudu-kudu, cewa an fasa yin taron.
KU KARANTA: Kiran 'yar majalisa karuwa: Alkali ya aike da dan majalisa gidan yari
Okowa ya ce hakika ba a mutunta mutanen yankinsu ba, an wulakanta su kuma ba a daraja su ba.
A cewarsa, yankin kudu-kudu, yanki ne mai matukar muhimmanci a kasar nan, an tozarta gwamnoninsu, ya kamata a ce an bai wa har shugabannin gargajiyarsu hakuri.
Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya wallafa hakan ne a shafinsa na Twitter, inda yace gaskiya ya kamata fadar shugaban kasa ta fito fili, ta basu hakuri.
KU KARANTA: An gwangwaje mutumin da yayi wa Buhari tattaki da kyautar mota da makuden kudi
A wani labari na daban, majalisar tarayya, kwamitin kungiyar yakin neman zaben Buhari na 2019, ta musanta zargin adana kayan tallafin COVID-19 da aka bada don raba wa 'yan Najeriya.
A cewar majalisar, babu wani sanata da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bai wa kudi ko kuma kayan tallafin COVID-19, Vanguard ta wallafa.
Sun gode wa shugaban kwamitin yada labarai da kamfen din Buhari, Engr. Kailani Muhammad, da yayi gaggawar sanar da su abinda ake ciki, inda suka ce babu wani dan majalisa da aka bai wa kayan tallafin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng