Kyan ki bai kai yadda nake so sirikata ta kasance ba, Mahaifiyar saurayi ga budurwa

Kyan ki bai kai yadda nake so sirikata ta kasance ba, Mahaifiyar saurayi ga budurwa

- Uwar saurayin da zan aura ta hanani aurensa, saboda ba ni da kyau, cewar wata budurwa

- Duk da budurwar tana dauke da cikin saurayin wata uku, don har baiko an kawo gidansu

- Ta nemi ta zubar da cikin, amma saurayin ya ki yarda, ya ce kada ta kuskura ta yi hakan

Wata budurwa wacce take dauke da cikin saurayinta, tana cikin tashin hankali, bayan mahaifiyar saurayin ta ce ba za ta taba barin ta ta auri danta ba saboda bata da kyau.

Budurwar, mai shekaru 28 da haihuwa, duk da ba ta so a bayyana sunanta ba, ta bai wa Arike Ade Pheonix labarin damuwarta don neman shawarar jama'a.

Kamar yadda tace, har saurayin na ta ya kai baiko gidansu, jaridar The Nation ta wallafa.

Sai dai, mahaifiyar saurayin ta ce ba za ta amince a yi auren ba saboda nisa da kuma munin budurwar.

KU KARANTA: 'Yan sanda ba za su cigaba da kalmashe hannuwa ana kashesu kamar kaji ba, kwamishina

Kyan ki bai kai yadda nake so sirikata ta kasance ba, Mahaifiyar saurayi ga budurwa
Kyan ki bai kai yadda nake so sirikata ta kasance ba, Mahaifiyar saurayi ga budurwa. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

Iyayen saurayin 'yan jihar Anambra ne, ita kuma budurwar 'yar jihar Enugu ce. Duk da dai akwai kiyayya ta musamman tsakanin jihohin guda biyu na gabas din Najeriya.

Yanzu haka, budurwar tana dauke da ciki wata 3, ta sanar da saurayin cewa za ta zubar da cikin saboda ba ta so ta haifi yaro ba tare da aure ba.

Amma saurayin ya murje idonsa, inda yace kada ta kuskura ta zubar, zai cigaba da kulawa da ita har ta haihu, ko da kuwa bai aureta ba.

KU KARANTA: Hotuna da bidiyon zukekiyar budurwar da Ned Nwoko zai aura a mata ta 7

A wani labari na daban, wani mutum dan Najeriya, mai amfani da suna Tare Brisibe, ya janyo maganganu a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, inda ya wallafa hotunan aurensa da matarsa 'yar kasar Romania.

Ya yi wa hotunan take da "idan ka samu kuma ka damke", ya wallafa hotunansa da matarsa wanda suka sanya takunkumi.

Duk da dai 'yan Najeriya da dama sun yi ta cewa ya yi auren ne don samun damar zama a kasar, babu wata soyayya, wasu kuma suna cewa soyayya ce.

Mutane da dama sun yaba yadda sutturar da ya sanya tayi masa kyau, a kalla ya samu mutane 15,000 da suka yaba da hotunan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel