Allah ya yiwa mahaifin Sheikh Albany Zaria, Malam Adamu, rasuwa

Allah ya yiwa mahaifin Sheikh Albany Zaria, Malam Adamu, rasuwa

Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Raaji'un! Allah ya yiwa mahaifin marigayi Sheikh Auwal Albany Zariya rasuwa, Sheik Dr Isa Ali Ibrahim, ya bayyana.

Dr Isa, wanda shine ministan sadarwa, ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook da safiyar Laraba, 18 ga watan Nuwamba, 2020.

Ya bayyana cewa marigayin ya rasu ne yau Laraba.

Ya yi addu'an Allah ya jikansa da rahama da kuma dukkan iyayenmu da malamanmu.

A cewarsa: "Allah Ya jikan mahaifin marigayi Shaykh Muhammad Auwal Adam Albani Zaria, Wato Malam Adamu. Yau Allah Ya dauki rayuwarsa."

"Allah Ya jikan dukkan iyayenmu da malamanmu, sannan Ya kyautata namu bayan na su."

Allah ya yiwa mahaifin Sheikh Albany Zaria, Malam Adamu, rasuwa
Allah ya yiwa mahaifin Sheikh Albany Zaria, Malam Adamu, rasuwa
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel