Kiran 'yar majalisa karuwa: Alkali ya aike da dan majalisa gidan yari
- Cece-kuce ya barke, bayan an yankewa wani dan majalisa hukuncin zaman gidan gyaran hali
- An yanke wa Hercules Okoro hukuncin ne sakamakon zarginsa da akeyi da cin zarafi
- Kotu ta zargesa da cin zarafin mataimakiyar kakakin majalisa, duk da ya musa zargin
An yankewa dan majalisar jihar Imo, Hercules Okoro, mai wakiltar mazabar Ohaji Egbema, hukuncin zama a gidan gyaran hali akan laifin cin zarafi.
Legit.ng ta tattara bayanai akan yadda aka kama Okoro, dan majalisa a karkashin jam'iyyar APC, a ranar 13 ga watan Nuwamba, bayan wani rikici da ya barke tsakaninsa da mataimakiyar kakakin majalisar tarayya, Amarachi Iwuanyanwu.
An adana Okoro a gidan gyaran halin ne saboda laifuka 8 da ake zarginsa da aikatawa. Duk da dai bai amsa laifin da ake zarginsa da su ba.
Duk da lauyansa, Amandibuogu Osondu ya nemi belinsa amma abin yaci tura. A cewarsa laifin bai kai a dauresa ba. Alkalin, T Okee yace zai bukaci wani lokaci kafin ya duba yuwuwar bayar da belinsa.
KU KARANTA: Bani da budurwa saboda mata suna tsoron tsayi na, matashi mai kammala hidimar kasa
KU KARANTA: 'Yan sanda ba za su cigaba da kalmashe hannuwa ana kashesu kamar kaji ba, kwamishina
A wani labari na daban, karamin ministan fetur, Timipre Sylva, ya ce tashin farashin man fetur ya auku ne saboda wani kamfanin hada magunguna na Amurika, Pfizer ya bayyana riga-kafin cutar COVID-19.
Sylva ya fadi hakan ne a wata ganawar sirri da yayi da shugaba Muhammadu Buhari a Abuja ranar Lahadi, inda ya sanar da manema labarai cewa samun riga kafin cutar COVID-19 shine sanadiyyar tashin kudin man fetur a kasuwannin duniya.
"Tashin farashin man fetur ya auku ne sakamakon sanar da riga-kafin cutar COVID-19 da Pfizer sukayi. Idan an lura, farashin ya karu ne bayan sanar da samuwar riga-kafin" yace.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng