Ba mu samu kudi ko kayan tallafin korona daga Buhari ba, Sanatoci

Ba mu samu kudi ko kayan tallafin korona daga Buhari ba, Sanatoci

- Majalisar tarayya ta wanke kanta daga zargin da jama'a suke yi mata

- Ta ce Shugaba Buhari bai ba ta kayan tallafin COVID-19 ba

- Ta ce babu kwabo ko tiyar shinkafa da shugaban kasa ya bata

Majalisar tarayya, kwamitin kungiyar yakin neman zaben Buhari na 2019, ta musanta zargin adana kayan tallafin COVID-19 da aka bada don raba wa 'yan Najeriya.

A cewar majalisar, babu wani sanata da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bai wa kudi ko kuma kayan tallafin COVID-19, Vanguard ta wallafa.

Sun gode wa shugaban kwamitin yada labarai da kamfen din Buhari, Engr. Kailani Muhammad, da yayi gaggawar sanar da su abinda ake ciki, inda suka ce babu wani dan majalisa da aka bai wa kayan tallafin.

A cewar majalisar, ko tiyar shinkafa basu gani ba, sannan ko sisi ba a raba mu su ba, balle su adana.

Kamar yadda majalisar ta saki wata takarda a ranar Litinin a Abuja, wacce shugaban kwamitin yada labarai, Sanata Ajibola Basiru ya saka hannu, sun ce a daina shafa musu kashin kaji.

A cewar majalisar, ba rabin albashinsu kadai su ka bayar ba, har raba wa mutane kayan tallafi suka yi daga aljihunsu, duk don taimakon wadanda suka yi laushi lokacin da ake ganiyar annobar COVID-19.

Majalisar ta kara da cewa, ba su ga dalilin da zai sa Kilani Mohammed ko kuma wani ya zargesu da wannan laifin ba.

KU KARANTA: Hotuna da bidiyon zukekiyar budurwar da Ned Nwoko zai aura a mata ta 7

Ba mu samu kudi ko yana tallafin korona daga Buhari ba, Sanatoci
Ba mu samu kudi ko yana tallafin korona daga Buhari ba, Sanatoci. Hoto daga @Vangudardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Babban abun alheri da ya taba samun Najeriya shine PDP, Atiku

A wani labari na daban, Kwamishinan 'yan sandan jihar Edo, Johnson Kokumo, ya ce 'yan sanda ba za su cigaba da kalmashe hannu 'yan ta'adda su na kashesu kamar kaji ba.

A ranar Litinin, Kokumo ya fadi hakan a wani taro na kaddamar da kungiyar 'yan sa kai 70 a karamar hukumar Ikopaba-Okha da ke jihar.

Ya bayyana asalin manufar zanga-zangar EndSARS, inda yace dan sa ya kashe kansa bayan masu zanga-zangar sun janyo masa asarar naira miliyan 7.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel