Hotuna da bidiyon zukekiyar budurwar da Ned Nwoko zai aura a mata ta 7

Hotuna da bidiyon zukekiyar budurwar da Ned Nwoko zai aura a mata ta 7

- Biloniyan nan, Ned Nwoko, mijin Regina Daniels yana shirin auren matarsa ta 7

- Ned yana shirin auren wata Sara, mazauniyar Ingila, mai kyau da diri

- Majiya mai karfi ta tabbatar da shirye-shiryen auren Ned da Sara bisa al'ada

An gano cewa mijin Regina Daniels, wacce ta bar kyakkyawan saurayinta ta auri tsohon biloniya kuma dan siyasa, Ned Nwoko, yana shirin kara aure.

An saka ranar auren Ned Nwoko da wata hadaddiyar budurwa mazauniyar Ingila, a matsayin matarsa ta 7.

Budurwar mai suna Sara, mai amfani da suna 'Sar8al' a kafar sada zumunta ta Instagram, ta zo Najeriya inda tayi 'yan kwanaki.

Hotuna da bidiyon zukekiyar budurwar da Ned Nwoko zai aura a mata ta 7
Hotuna da bidiyon zukekiyar budurwar da Ned Nwoko zai aura a mata ta 7. Hoto daga Reginadaniels
Asali: Instagram

Idan ba a manta ba Ned Nwoko ya auri Regina Daniels a matsayin matarsa ta 6 a 2019, bayan soyayya mai zurfi da suka sha, har ta haifi santalelen jariri a shekarar 2020.

Hotuna da bidiyon zukekiyar budurwar da Ned Nwoko zai aura a mata ta 7
Hotuna da bidiyon zukekiyar budurwar da Ned Nwoko zai aura a mata ta 7. Hoto daga Reginadaniels
Asali: Instagram

KU KARANTA: Bidiyon mace mai sana'ar jan babbar mota ya janyo cece-kuce

Regina Daniels ta dade tana saka hotunanta tare da bidiyoyin budurwar a Instagram da Snapchat, wanda aka ga a hannun budurwar da zoben sa rana, kuma ta kan yi tsokaci a kai da "Matarmu".

Hotuna da bidiyon zukekiyar budurwar da Ned Nwoko zai aura a mata ta 7
Hotuna da bidiyon zukekiyar budurwar da Ned Nwoko zai aura a mata ta 7. Hoto daga Reginadaniels
Asali: Instagram

An ga Regina Daniels a Abuja, cikin ranakun karshen mako tare da Sara suna wanka a wani bangare na gidan Ned Nwoko.

Sannan an ga bidiyon da Regina da ita suke cikin tankamemiyar mota suna shakatawa, wanda Sara ta wallafa, amma yanzu ta goge.

Majiya daga cikin gidan Ned ta tabbatar da cewa yanzu haka sunata shirye-shirye irin na al'ada akan auren.

KU KARANTA: Tabbas na yi lalata da jikata, amma ban san ta samu ciki ba, tsoho mai shekaru 70

A wani labari na daban, dan dagacin wani kauye ya rasa ransa sakamakon rikicin jami'an kwastam da wasu matasa 'yan sumogal a jihar Kebbi., jaridar The Punch ta wallafa.

Rikicin ya hargitse tsakanin jami'an kwastam na Kaduna da suke aiki a jihar Kebbi, da wasu matasa, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar wani saurayi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng