Bani da budurwa saboda mata suna tsoron tsayi na, matashi mai kammala hidimar kasa

Bani da budurwa saboda mata suna tsoron tsayi na, matashi mai kammala hidimar kasa

- Wani saurayi, mai suna Cardoso Oluwatosin Michael, ya ce ya kasa samun matar aure saboda bala'in tsayinsa

- Cardoso wanda tsayinsa ya kai kafa 6.9, ya ce kashi 60 cikin dari na 'yan matan da yake so sun rabu da shi saboda tsayinsa

- A cewarsa, yana fuskantar kalubale saboda tsayinsa, wasu gani suke yi kamar ba mutum bane shi

Allah mai halitta iri-iri, wasu masu kiba, wasu sirara, wasu kuma dogaye wasu gajeru. Cardoso Oluwatosin Michael, dan jihar Lagos bai dade da gama bautar kasarsa ba a Minna, jihar Niger.

Cardoso ya gama karatunsa a Polytechnic din jihar Ibadan, inda yayi karatu a kan harkokin gwaje-gwajen asibiti a 2018.

Yanzu yana shirin samun mata ne ya aura, wacce za su wuce kasar waje don ya cigaba da karatunsa. Sai dai yana da wata matsala.

Babbar matsalar da yake fuskanta shine samun mata wacce za ta aureshi duk da bala'in tsayinshi.

A wata hira da aka yi da shi, mutum ne mai barkwanci, wanda yayi bayani a kan rayuwarsa, iyayensa, da sauransu.

Tsayinsa ya kai kafa 6.9, kuma babban burinsa shine ya zama malamin jami'a. Sananne ne shi a harkar wasan kwallon raga. Wanda tsayinsa ya taimaka masa wurin yin kwallonsa cikin kwanciyar hankali.

An tambayeshi idan shi ne wanda yafi kowa tsayi a Najeriya, inda yace gaskiya bai sani ba, saboda bai zagaye Najeriya ya duba ba. Duk da dai duk inda yaje, yafi kowa tsayi.

A cewarsa, iyayensa suna da tsayi daidai gwargwado, kawai shine dai Allah yayi a haka. Amma akwai wani kawunsa mai tsayi sosai, yana tunanin a wurinsa ya gado.

Ya ce akwai ranar da yaje shiga mota, direban ya hana shi shiga, saboda yana tunanin ko aljani ne shi, Vanguard ta wallafa.

Hatta kayan da yake saka wa, tsayinsu yana wuce misali. Ba ya iya siyan kaya, sai dai ya siyo yadi a dinka masa, takalma kuma yana da mutumin da yake nemo masa.

Yace yana da burin auren matar da tsayinta ya kai kafadarsa, ko kuma bata kai ba da kadan, yadda abin zai tafi daidai. Amma yanzu bashi da budurwa, saboda a kalla kaso 60 cikin dari na 'yan matan da ya hadu da su, sun gudu ne saboda tsayinsa.

KU KARANTA: FG ta shiga matukar damuwa a kan barkewar cutar zazzabin Lassa

Bani da budurwa saboda mata suna tsoron tsayi na, matashi mai kammala hidimar kasa
Bani da budurwa saboda mata suna tsoron tsayi na, matashi mai kammala hidimar kasa. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Shugaban karamar hukuma ya lallasa wa mai neman kujerarsa mugun duka

A wani labari na daban, ana zargin shugaban karamar hukumar Gaya da ke jihar Kano, Ahmad Abdullahi Tashi, da Shu'aibu Gamarya, shugaban majalisar kansilolinsa, da yi wa mai neman kujerarsa, Hafizu Sunusi Mahmoud Gaya, dukan tsiya.

Al'amarin ya faru ne daidai lokacin da 'yan siyasan suke fafutukar ganin sun samu nasarar cin zaben da za'ayi na kananan Hukumomi a watan Janairun 2021.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng